1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A na shirin hawa tebrin shawara tsakanin yan tawaye da gwamnatin Burundi

Yahouza SadissouMarch 15, 2006

Yan tawayen FNL na Burundi, sun yi tayin hawa tebrin shawara da gwamnati

https://p.dw.com/p/Bu19
Hoto: AP

Madugun yan tawayen Hutu na Burundi, ya yi tayin hawa tebrin shawara da gwammatin wannan kasa.

Agathon Rwasa, yayi bayana wannan sanarwa, a yayin da ya kiri wani taron manema labarai, a birnin Dar Es Salam na Tanzania.

Saidai ya bayyana damuwa, a game da yada gwamnati ke ci gaba, da aikata kissan gilla, ga magoyan bayan ƙungiyar tawaye FNL, wacce a halin yanzu ita kaɗai ke da saura, a jerin ƙungiyoyin tawaye da Burundi ta yi fama da su, a tsawan shekaru 12.

A halin da ake ciki ,shugaban yan tawayen FNL ya koka da cewa a ƙalla mutane 5000, ke tsare gidajen kurkuku, kokuma a ka ganawa azaba, saboda dalilin goyan baya da su ke baiwa kungiyar tawayen FNL.

Ministan harakokin wajen Tanzania, da ya karɓi baƙuncin shugaban rundunar tawayen, ya ce ƙasar sa, a shire take, ta bada haɗin kai, don warawre rikicin Burundi.

Tun watan janairu da ya wuce, gwamnatinTanzania, da ke daya daga ƙasashen masu shiga tsakanin rikicin Burundi, ta gabatarwa hukumomin Bujumbura, wata sabuwar taswirar samar da zaman lahia ,ta hanyar shawarwari da yan tawayen FNL, wanda har ya zuwa yanzu, su ka nuna kin amincewa da sabuwar gwamnatin Burundi.

A wata sanarwa da ta hido jiya, gwamnatin ta ce a shire ta ke, ta hau tebrin shawarwarin,amma da sharaɗin ƙasashe masu shuga tsakani sun buƙaci hakan.

Kakakin gwamnatin Burundi, Karenga Ramadhani ,ya buƙaci Tanzania, ta gabatar da shawarwarin na ta, ga shugaban ƙasar Uganda Yoweri Museveni ,wanda ke matasayin shugaban komitin sassanta rikicin Burundi.

A na sa gefe, shugaban ƙasar Burundi, Pierre Nkurunziza, ya bayyana shakku ga wannan sabuwar aniya ,da yan tawayen su ka nuna.

Ya ce idan lalle da gaske su ke, to yi mubai ´a ga sabuwar gwamnati.

A shekara bara ne, Burundi ta shirya zabbuka daban daban wanda su ka bata damar fita daga shekaru 12 na yaƙin bassasa.