1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Najeriya an ɗage Dokar hana yawon Dare a birnin Jos

May 20, 2010

Jihar Plato dai tayi fama da rikicin addini dana ƙabilanci da kuma na Siyasa tsakanin musulmi da kirista

https://p.dw.com/p/NSPm
Wani gida da aka ƙona a rikicin JosHoto: AP

Rahotannin dake fitowa daga Jos babban birnin jihar Plato da tayi fama da rikicin ƙabilanci dana addini na cewar gwamnatin jihar ta ɗage dokar hana yawon dare da aka ƙaƙabawa birnin tun a shekara ta 2008 bayan ɓarkewar rikicin addini dana ƙabilanci daya laƙume ɗaruruwan rayukan al'umma.

Kanfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito kwamishinan yaɗa labaran jihar Gregory Yenlong na sanar da ɗage dokar a wani jawabi ta gidan radiyon jihar. Yanzu haka dai gwamnatin tarayyar ƙasar ta kafa wani kwamiti domin gano musabbabin rikicin jihar ta Plato da ake dangantawa da Siyasa.

Shugabannin addinai na Kirista da musulmi sun sha zaman tattaunawa da nufin samun zaman lafiya a jihar baki ɗaya. Rikicin addini kona ƙabilanci na ɗaya daga cikin matsalolin dake haifar da rikici a wannan ƙasa mai mutane fiye da miliyan 140 da kuba ƙabilu fiye da 300.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Umaru Aliyu