1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A Rangoon an girke dakaru da ´yan sanda a wuraren ibada na ´yan Bhudda

September 26, 2007
https://p.dw.com/p/BuAF

Gwamnatin mulkin sojin kasar Burma ta umarci dakaru da ´yan sandan kwantar da tarzoma da su kasance a wuraren ibada na ´yan Bhudda don dakatar da zanga-zangar gama gari ta kin jinin gwamnati. Hakazalika hukumomin kasar sun kafa dokar hana fitan dare sannan sun haramta yin gangami a wani mataki na hana maimacin jerin zanga-zanga da maci dubban mutane akan tituna. Rahotanni sun ce an kame mutane da dama musamman wadanda suka shirya macin nuna adawa da gwamnatin sojin wanda shine irin sa mafi girma cikin shekaru 20. Kawo yanzu shugabannin sojin kasar ba su yi amfani da karfi don murkushe zanga-zangar ba amma an girke sojoji a cikin damarar yaki a sassa daban daban na birnin Rangoon. A irin wannan rikici da aka fuskanta a shekarar 1988 gwamnati ta halaka dubban mutane wadanda suka shiga wata zanga-zanga da dalibai suka jagoranta.