1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

November 20, 2009

Bayan ɗari-ɗari na tsawon shekaru a wannan makon mahukuntan Jamus sun tasa ƙeyar madugun 'yan tawayen Hutu da muƙarrabinsa zuwa gidan waƙafi

https://p.dw.com/p/KcAL
Madugun 'yan tawaye Ignace MurwanashyakaHoto: picture-alliance/ dpa

Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kannun rahotannin jaridun Jamus akan al'amuran Afirka a wannan makon shi ne cafke shuagabannin ƙungiyar 'yan tawayen ta FDLR mai gudanar da ayyukanta a janhuriyar demoƙraɗiyyar Kongo da aka yi a nan Jamus. A cikin nata rahoton jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

"Bayan ɗari-ɗari da ofishin lauya mai ɗaukaka ƙara na tarayyar Jamus ya daɗe yanayi a game da ba da umarnin cafke mutanen biyu bisa zargin aikata miyagun laifuka na yaƙi, bisa iƙirarin cewar shi ma tsofon sakataren tsaron Amirka Donald Rumsfeld da tsofon ministan cikin gida na Uzbekistan Zakiriyon Almatov, ba ɗaya daga cikinsu da aka gufanar gaban kuliya duk da ƙarar da ƙungiyoyin kiyaye haƙin ɗan-Adam suka ɗaukaka kansu. Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam dai sun sha sukan lamirin mahukuntan Jamus akan irin wannan ɗariɗari da suke wajen kame masu miyagun laifuka na yaƙi."

Ita kuwa jaridar Neues Deutschland cewa tayi:

"Ga 'yan Afirka da dama, musamman ma ga mazauna yankin gabacin janhuriyar demoƙraɗiyyar Kongo, labarin kame madugun 'yan tawayen ƙungiyar Hutu ta FDLR Ignace Murwanashyaka da mataimakinsa Straton Musoni, shi ne wani labari mafi daɗi da suka samu tun lokaci mai tsawo. Tun dai a shekara ta 2005 Majalisar Ɗinkin Duniya ta saka Murwana shyaka cikin jerin masu laifukan ke ta haddin ɗan-Adam a yaƙi, amma ya ci gaba da zamansa a Jamus, gabansa gaɗi. Amma al'amura sun canza a ranar talatar da ta shige, inda mahukunta suka cafke shi suka kuma tasa ƙeyarsa zuwa waƙafi bisa zarginsa da aikata miyagun laifuka na yaƙi da cin zarafin ɗan-Adam."

Ƙasar Malawai na ɗaya daga cikin ƙasashen ƙalilan da suka samu kafar bunƙasa ayyukan noma, inda a baya ga kafar da take da wajen ci da al'umarsu take kuma da ikon fitar da masara zuwa ƙetare. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ce ta ba da wannan rahoto, inda take cewar:

Malawi Soziale Sicherheit Orangenverkäuferinnen
Bunƙasar noma a MalawiHoto: DW

"Ƙasar Malawi na daga cikin ƙasashen Afirka da suka cancanci yabo da zama abin koyi dangane da rawar da ta taka wajen yaƙi da matsalar yunwa. Ƙasar wadda a shekara ta 2005 ta sha fama da matsdalar fari ta kuma dogara wajen shigo da kashi ɗaya bisa shida na masarar da take buƙata daga ƙetare, a yanzu ta wayi gari tana da ikon samar da rarar masara ta kimanin tan miliyan ɗaya da dubu nɗari uku da take fitarwa zuwa ƙetare. Wannan ci gaban kuwa ya samu ne sakamakon rawar da gwamnati ta taka wajen karya farashin taken da manoma ke buƙata don samar da amfani mai yalwa."

Sai dai kuma lamarin ya banbanta dangane da ƙasar Muzambik dake samun taimakon kashi 50% daga ƙetare don cike giɓin kasafin kuɗinta a cewar jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ci gaba da cewar:

Pemba Feld Afrika Mosambik
Ƙasar Muzambik bata samun ci gaba ga tattalin arziƙintaHoto: Wikipedia

"Babban abin takaici game da wannan taimakon da ake bayarwa shi ne kasancewar al'umar ganin basa gani a ƙasa, kuma wannan shi ne ainihin dalilin da ya sanya ƙasar har yau take cikin jerin ƙasashe goma da suka fi fama da talauci a duniya, duk kuwa da alƙaluman da ake bayarwa game da bunƙasar kashi takwas cikin ɗari na jumullar abubuwan da Muzambik ke samarwa a shekara."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Umaru Aliyu