1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A ranar za a kada kuri'a kan matakin tsige Shugaba Zuma

Mohammad Nasiru Awal ATB
August 7, 2017

'Yan adawa a Afirka ta Kudu sun yi kira ga wakilan jam'iyyar ANC da su kada kuri'ar yankan kauna ga Shugaba Jacob Zuma.

https://p.dw.com/p/2hqBd
Südafrikaner fordern Präsident Zuma zum Rücktritt auf
Hoto: Reuters/S. Sibeko

Manyan jam'iyyun adawa a kasar Afirka ta Kudu wato Democratic Alliance da kuma Economic Freedom Fighters sun yi kira ga 'yan majalisar dokoki na bangaren jam'iyyar ANC da ke mulki da su kada kuri'ar tsige Shugaba Jacob Zuma da za a yi a ranar Talata.

Sun yi wannan kira ne bayan da shugabar majalisar dokokin Afirka ta Kudu, Baleka Mbete, wadda 'yar ANC ce, ta yanke hukuncin cewa za a kada kuri'ar ce a asirce.

Julius Malema shi ne shugaban jam'iyyar Economic Freedom Fighters da ya yi karin haske.

Ya ce: "Ba su da wata hujjar tursasawa ko zargi. Mun fafata saboda dukkan membobin majalisa ciki har da na ANC da na 'yan adawa da suka rika tursasa wa membobinsu suna tilasta musu da su goyi bayan Shugaba Zuma. Wannan nasara ce ga adawa, nasara ce ga Afirka ta Kudu, nasara ce kuma ga tsarin mulki."

A wannan Talata majalisar dokokin za ta kada kuri'a kan wani mataki wanda in ya yi nasara, to Zuma da majalisar ministocinsa za su sauka daga kan karagar mulki.