1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yanzu haka dai sabon shugaban hukumar EU mai jiran gado yace zai sake gabatra da sunaye mutanen da yake son a nada kan ministocin hukumar--

Jamilu SaniOctober 27, 2004

Barroso yace zai tuntubi shugabin Eu da majalisa kafin ya sake gabatar da sabin sunayen ministocin hukumar Eu---

https://p.dw.com/p/Bvf7
Hoto: dpa

Sabon shugaban hukumar kungiyar hadin kann turia mai jiran gado ya janye shawarar da ya gabatar ta nadin sabin manyan jami’an hukumar,don kada hakan ya musugunawa majalisar kungiyar hadin kann turia kuma ya haifar da matsaloli na rudanin siyasa a cikin kungiyar.

Bugu da kari sabon shugaban hukumar ta kungiyar hadin kann turia mai jiran Gado Jose Manuel Barosso ya shaidawa yan majalisar kungiyar hadin kann turia sa’a daya kafin a cimma kudiri kann nadin sabin jami’an hukumar kungiyar hadin kann turia cewar,ya kamata ya janye shawarar da ya gabatarwa majalisar ta neman a amince da nadin manyan jami’an hukumar saboda yin hakan zai zama mai alfanu ga cigaban kungiyar hadin kann turia ba.

Barroso ya fuskanci adawa ne daga yan majalisar kungiyar hadin kann turia,bayan da ya zabi Rocco Buttiglione a matsayin sabon ministan sharia da kuma tsaro na hukumar ta kungiyar hadin kann turia,mutumin kuma da yan majalisar kungiyar hadin kann turia suka zarga da laifin yin amfanin tsatsauran ra’ayinsa na yan Roman Katolika wajen sukan lamirin masu ra’ayin aurataya ta jinsi daya.

Tsohon Pm kasar ta Portugal ya shaidawa yan majalisar kuniyar hadin kann turia cewar,zai tuntubi shugabanin kungiyar Eu,da kuma majalisa kafin ya sake gabatar da sunayen mutanen da yake son nadawa a matsayin manyan jami’an hukumar kungiyar hadin kann turia nan da yan makoni masu zuwa.Wanan tsaiko da za’a fuskanta na nadin sabin ministocin hukumar kungiyar hadin kann turia,zai sanya Shugaba mai barin gado Romani Prodi dan asalin kasar Italiya ya cigaba da zama kann mukaminsa har sai abinda hali yayi,kamar dai yadda kasar Netherland dake rike da shugabancin kungiyar hadin kann turia ta shaidawa yan majalisar kungiyar hadin kann turia.

Mai magana da yawun hukumar kungiyar hadin kann turia Reijo Kemppinenen ya baiyana cewar Prodi ya amince ya cigaba da zama kann mukaminsa,bayan da PM kasar Netherland Jan Peter da kasarsa ke rike da shugabancin kungiyar hadin kann turia ya bukaci shi da yayi hakan.

Shugaban majalisar kungiyar hadin kann turia Josep Borrell ya baiyana cewar wanan jinkiri da aka samu na nadin sabin ministocin hukumar kungiyar hadin kann turia,abu ne ya kawo cikas ga cibaban aiyukan kungiyar hadin kann turia.

Abinda har yanzu ba’a sanni ba shine ko Barroso zai yi gayara game da nadin sabin ministocin hukumar kungiyar hadin kann turia su 25 da ya riagaya ya gabatar,ko kuwa zai baiwa kasahen dake cikin hukumar damar zabar mutum mutumin da suka da dace a nada shi a matsayin mukamin minista a hukumar ta kungiyar hadin kann turia.