1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau ake bikin ranar ma'aikata ta Duniya

May 1, 2010

Rundunar 'Yansandan jamus tasha alwashin hukunta masu tada husama a lokacin bikin ranar ma'aikata a birnin Berlin

https://p.dw.com/p/NC1C
'Yan sandan kwantar da tarzoma a fito na fito da masu zanga-zanga a birnin BerlinHoto: AP

Rundunar 'yansandan Jamus tasha alwashin sa ƙafar wando ɗaya da duk masu tada rigima a lokacin bikin ranar ma'aikata da ake gudanar yau ɗin nan a Birnin Berlin.

Babban Jami'in Yan sandan ƙasar Konrad Freiberg yace 'yansanda ba zasuci gaba da zura ido akan wasu gungun jama'a dake neman tada husuma na haifar da hasarar duniyar jama'a dana gwamnati a duk shekara wajen wannan biki ba.

Kanfanin dillancin labaran AP ya ruwaito shugaban 'yan sandan na cewa a bara kaɗai 'yan sanda 470 ne aka jiwa rauni sakamakon bata kashi tsakanin su da masu zanga-zanga.

Tuni dai aka baza 'yansandan a sassa daban-daban na birnin Berlin da kuma wasu jihohin anan Jamus da aka saba gudanar da wannan fito na fiton.

A bana dai bikin ranar ma'aikatan a sassan duniya daban-daban zai fuskanci fushin ma'aikata ne a sakamakon matsalar tattalin arziki da ƙasashen duniya suke fuskanta.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita:Yahouza Sadissou Madobi