1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau ake rantsar da Joseph Kabila

December 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuZ1

A yau ne ake rantsar da Joseph Kabila a matsayin shugaban kasa a zabe karo na farko da akayi cikin yanci a jamhuriyar demokradiyar Kongo.

Yayinda ake shirin rantsar da shugaban a yau,a jiya tashe tashen hankula sunci gaba tsakanin dakarun gwamnati da yan tawaye karkashin jagorancin janar Laurent Nkundu da yayiwa sojin kasar tawaye.

Dakarun na Nkundu sun kame kauyen Runyoni dake arewa maso gabashin birnin Goma.

A halinda ake ciki kuma ofishin MDD a Goma ya sanarda cewa,yan gudun hijira daga yankin Sake wadanda suka koma gida bayan gujewa fada a makon daya gabata sun taraddda dukkan gidajen nasu a rushe bayan tashe tashen hankula tsakanin yan tawaye da sojojin gwamnati.