1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau ake zaben shugaban kasa a Finnland

January 15, 2006
https://p.dw.com/p/BvCF

A yau al´umar kasar Finnland ke zaban sabon shugaban kasa don yin wani sabon wa´adi na shekaru 6. Masu kalubalantar shugaba mai ci kuma ´yar takarar jam´iyar Social Democrat Tarja Halonen, sun hada da tsohon ministan kudi kuma mai ra´ayin mazan jiya Sauli Niinisto da kuma FM Matti Vanhanen. Binciken jin ra´ayin jama´a ya nunar da cewa shugaba Halonen ke kan gaba da kimanin kashi 50 cikin 100. Idan ta gaza samun wannan adadi na kuri´u to za´a yi zagaye na biyu na zaben a ranar 29 ga watannan na janeru, inda zata fuskanci wanda ya zo na biyu a zaben na yau lahadi.