1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau hukumar IAEA zata bada rahotanta kan shirin nukiliya na Iran

Hauwa Abubakar AjejeApril 28, 2006

Saoi kadan kafin hukumar kare yaduwar makaman nukiliya ta IAEA ta mika rahotanta akan shirin nukiliya na Iran,shugaba Ahmedinajad yace,kasarsa zata yi watsi da duk wani matsin lamba dangane da dakatar da inganta sinadarin uranium

https://p.dw.com/p/Bu0Q
Ahmedinajad
AhmedinajadHoto: AP

Akwai dai alamun cewa,shugaban hukumar ta IAEA,Muhammad al-Baradei zai bada rahoton cewa,har yanzu kasar Iran bata nuna alamun zata bi umurnin da hukumar ta bata ba,yayinda waadin da aka diba mata na kwanaki 30 ya kawo karshe.

Iran din dai a nata bangare sai kara yin watsi takeyi da wannan batu,musamman ma kara inganta sinadarin uranium da tace tayi,tare kuma da bincike da takeyi akan wata naura da zata iya sarrafa sinadarin na uranium cikin gaggawa,tana mai cewa iata fa ba gudu ba ja da baya a wannan yunkuri nata.

Kwanaki biyu kafin rahoton na yau,Iran ta sha alwashin zata kai hare hare kan duk wasu bukatu na Amurka a koina cikin duniya,muddin dai Amurka ta kai mata hari,batu da Amurkan take duba yiwuwarsa a zaman mataki na karshe idan Iran din ta ci gaba da nuna taurin kai.

Hakazalika jakadan kasar Iran a Majalisar Dinkin Duniya Javad Sharif,yace,Iran ba zata amince da wani kudiri na komitin sulhu da bata amince da shi ba,saboda a cewarsa,shirin nata na nukiliya bai kasance wani barazana ga zaman lafiya na duniya ba.

Taron ministocin harkokin wajen kungiyar tsaro ta NATO a Sofia,yayi kokarin shawo kan Rasha akan mataki da zaa dauka akan kasar ta Iran,saoi kadan kafin al Baradei ya mika rahotan nasa.

A yau ne dai ake sa ran ministan harkokin wajen kasar Rasha,Sergei Lavrov zai gabatar da jawabi ga takawarorinsa,saoi kadan kafin taron hukumar kare yaduwar nukiliya ta kasa da kasa inda al Baradei zai mika rahotan nasa.

A dai jiya alhamis ne shugaban kasar Iran Mahmud Ahmedinajad ya sha alwashin cewa kasar ba zata bada kai bori ya hau ba,game da abinda ya kira rashin adalci da matsin lamba na wasu kasashe.

Ministan harkokin wajen Jamus Frank Walter Steinmeire a taron NATO shima ya tofa albarkashin bakinsa game da shirin nukiliya na Iran.

sakatariyar harkokin wajen Amurka Condoleeza Rice,dai tace dole ne kasashe membobi su bi umurnin komitin sulhu.

Tace saboda kare martabarsa,ya kamata komitin sulhu ya dauki mataki,komitin sulhu,majalisa ce mai muhimmanci ga tabbatr da zaman lafiya da tsaro a duniya,kuma ba zai yiwu wata kasa memba tayi watsi da umurninsa ba.

Rasha da Sin,wadanda membobi dake da ikon darewa kujerar naki a komitin sulhu,a nasu bangare,sun ki bada hadin kai game da batun takunkumi.

Yayinda ake ci gaba da samun sabani tsakanin kasashen yammacin duniya game da batun nukiliya na Iran,hukumar IAEA dai taki furta wasu kalamai da zasu nuna tana goyon bayan wani bangare cikin wannan rikici.