1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau Kofi Annan ke fara ziyara a Iran

September 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bukn

A yau asabar babban sakataren MDD Kofi Annan zai kai ziyara birnin Teheran a ci-gaba da rangadin kasashen yankin GTT da yake yi. Wannan ziyarar ta zo ne kwanaki biyu bayan cikar wa´adin da kwamitin sulhu ya dibarwa Iran din ta dakatar da shirin sarrafa sinadarin uranium. Annan zai tattauna da mahukuntan kasar musamman game da shirinta na nukiliya da ake takaddama akai, sai kuma goyon bayan da Iran din ke bawa kungiyar Hisbollah. Don kauracewa matakan jan kunne na kwamitin sulhu, KTT ta ce tana goyon bayan ci-gaba da shawarwari don samun masalaha game da shirin nukiliya. A halin da ake ciki babban jami´in diplomasiya na EU Javier Solana zai gana da mai shiga tsakani a tattaunawar nukiliyar Iran Ali Larijani a mako mai zuwa. Su ma kasashen Rasha da China sun goyi da bayan ci-gaba da shawarwarin. Amma a nata bangaren Amirka na son a dauki matakin jan kunnen Iran saboda gaza cika wa´adin MDD na dakatar da shirin inganta karfen uranium.