1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau za´a fara shawarwarin kafa gwamnati a yankunan Falasdinawa

February 3, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9e
A yau shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da wakilan kungiyar masu kishin addinin Islama ta Hamas zasu gudanar da shawarwari a Zirin Gaza akan kafa sabuwar gwamnati. A zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinawa da aka gudanar a ranar 25 ga watan janeru, Kungiyar Hamas ta ka da kungiyar Fatah ta shugaba Mahmud Abbas, inda ta lashe kujeru 76 daga cikin 132 na wannan majalisa. Tuni dai magoya bayan kungiyar ta Fatah suka gargadi shugabanninsu da kada su kuskura su shiga cikin wata gwamnatin hadin guiwa da Hamas. Yanzu haka dai Hamas ta yi watsi da wasu sharudda da aka gindaya gabanin gudanar da shawarwarin kafa gwamnatin. Da farko Amirka da KTT sun yi kira ga Hamas da ta ajiye makamanta kana kuma ta amince da ´yancin wanzuwar Isra´ila a matsayin kasa.