1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abbas ya gamsu da ganawar da ya yi da Ehud Olmert

August 7, 2007
https://p.dw.com/p/BuER

Shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, ya bayyana gamsuwa da tanttanawar da yayi da Praministan Isra´ila Mahmud Abbas, wadda ta gudana yammacin jiya, a birnin Jericho, na gaɓar yamma ga kogin Jordan.

Abbas ya bayyana hakan, a lokacin da ya ke gabatar da jawabi ga Palestinawa, a game da sakamakon da taron ya cimma.

A cewar sa, wannan shine karon farko, da ɓangarorin 2 su ka cimma matsaya ɗaya a game da batutuwa masu mahimmanci.

Tun mako mai zuwa Isra´ila ta alƙawarta cire wasu shingaye da ta gitta, domin baiwa Palestinawa damar gudanar da zirga-zirga.

To saidai har yanzu, taron bai bayyana kamai ba, a game da batun iyakokin ƙasar Palestinu.

Saidai a ta bakin tsofan Praminista Isma´il Haniey, wanda ƙungiyar sa ta Hamas ke riƙe da zikin Gaza,taron na jiya ba yi nasara ba.

Mahalarta taron Jericho, sun tafi da burin masanyar ra´ayoyi, a game da wannan batu mai sarƙƙaƙiya, da zumar cimma matsaya guda, kamin watan november mai zuwa, wanda a cikin sa ne, Amurika ke sa ran kiran wani taron ƙasa da ƙasa, domin tanttana batun girka ƙasashe 2 na Isra´ila da Palestinu masu maƙwataka da juna cikin girma da arziki.