1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abdullah Gül ya yi rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban ƙasar Turkiya

August 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuCt

An rantsad da tsohon ministan harkokin wajen Turkiya Abdullah Gul a matsayin shugaban kasa na karo 11. A cikin jawabin kama aiki da yayi Gul yayi alkawarin girmama kundin tsarin mulkin Turkiya wadda babu ruwanta da addini. Hakan dai ta zo ne sa´o´i kalilan bayan yalashe zaben zagaye na uku a majalisar dokokin kasar. A zabuka guda biyu da aka gudanar da farko Gul ya gaza samun rinjayen kashi 2 cikin 3 da ya ke bukata. A kuma halin da ake ciki kasashen Turai sun yi maraba da zaben Gul din. A lokacin da yake tifa albarkacin bakinsa shugaban hukumar KTT Jose Manuel Barroso ya yi maraba da zaban tsohon ministan harkokin wajen na Turkiya Abdulah Gul a mukamin shugaban kasar. Barroso ya bayyana zaben da cewa zai karfafa kokarin da Turkiya ke yi na samun shiga cikin kungiyar EU.