1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abin fashewa ya raunata mutum 22 a Landan

Ramatu Garba Baba
September 15, 2017

Firaiministar Britaniya Theresa May ta ce za a ci gaba da karfafa tsaro a kasar bayan harin da aka kai da ya raunata mutane akalla 22.

https://p.dw.com/p/2k45J
London Explosion in Underground
Hoto: Getty Images/AFP/D. Leal-Olivas

Rundunar 'yan sanda a Britaniyan ta ayyana harin a matsayin na ta'addanci inda ta shawarci al'umma da su guji zuwa wurin da aka samu fashewar da ta haifar da rudani a tashar jirgin a yayin bincike gano wadanda suka kai wannan harin.

Magajin garin birnin Landan Sadiq Khan a jawabinsa ga manema labarai bayan aukuwar lamarin ya yi alla-wadai da abinda ya kira ayyukan muggan mutane da ke anfani da ta'addanci domin hana al'umma walwala, karo na biyar kenan da ake kai wa Britaniya hari a cikin wannan shekara ta 2017.