1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abrini ya ce ya na da hannu harin Brussels

Ahmed SalisuApril 9, 2016

Mutumin nan da ake zargi da hannu wajen kai hare-haren birnin Paris na Faransa a bara ya ce shi ne wanda ake nema dangane da harin da aka kai filin jirgin saman Brussels.

https://p.dw.com/p/1ISeW
Belgien Brüssel Anschlag Terror Verdächtiger Videostill
Hoto: picture-alliance/dpa/Belgian Federal Police

Mutumin mai suna Mohamed Abrini ya shaidawa hukumomi a Belguium din cewar shi ne mutum nan da ke tare da wasu mutum biyu da suka kai harin kunar bakin wake a filin jirgin saman wanda ya yi sanadin rasuwar mutane da dama.

Mai magana da yawun babban mai gabatar da karar ta Belgiyam ya ce Mr. Abrini ya amince cewar ya na da hannu a harin bayan da aka nuna masa hoton bidiyon da ya ke ciki sanye da malafa kana ya na tura wasu akwatuna jim kadan kafin kai harin.