1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Abubuwan ban Al'ajabi a Duniya

Abba BashirJanuary 23, 2006

Abubuwan da suka fi ban mamaki a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVb
Dalar Giza
Dalar Giza

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon, ta fitone daga hannun Malam Musbahu Jibrin ma zauni a legas Nijeriya. Malamin Ya ce don Allah ya na son a sanar da shi abubuwa 7 da suka fi ban mamaki a Duniya.

Amsa : To Malam Musabahu mai yasa baka fayyace tambayar taka ba, saboda kasancewar akwai nau’o’i daban-daban na abubuwan ban mamaki a Duniya, kama dai daga na Tarihi, na zamani da kuma na ikon Allah,wato ma’ana na ikon Allah shine, abubuwan da suke na ban al’ajabi daga tsarin halittar da Allah (SWT) ya yi musu. To Amma duk da haka zamu duba dukkan fannonin guda uku.

To bari mu fara da abubuwan ban mamaki na tarihi wadanda suka fi ban al’ajabi a Duniya,wadanda kuma ake kallonsu a matsayin wata fasaha da hikima ta Dam-adam wajen sarrafa abubuwan da Allah ya halitta a doron kasa. Duk da cewa su wadannan abubuwan ban al’ajabi sun wanzune a wani zamani mai nisa da ya shude, to amma koda wanda ya rayu a wancan zamani da abubuwan suka faru, dolene sai ya bukaci na’urori irin na zamani domin ya ganewa idonsa dukkan wadannan abubuwan ban mamaki guda 7 .Dagacikinsu dai, Dalar Giza da ke birnin Alkahira a Kasar Misra itace kadai tai saura, amma duk sauran a yanzu haka babu su sai dai tarihi, wadannan abubuwa kuwa sun hada da Hamshakin Lambunnan na Birnin Babila wanda aka fi sani da suna “The hanging gadens of Babylon” da Dakin Ibada na Artennis, wato “The temple of Artennis”a Turance, da Mutum-mutumin Zeus, wato “The Statue of Zeus” da Gidan Haske na Alexandria, wato “The Lighthouse of Alexandria” Sai ginin da aka ajiye gawar Halincarnassus, sai na bakwansu shine Katon Mutum-mutumin Rhodes, wanda aka fi sani da suna “The colossus of Rhodes” a turance. Kuma dukkan wadannan yanzu haka babusu a doron kasa saidai tarihi kawai da ya tabbatar da cewa sun taba wanzuwa a Duniya.

To ayayin da shida daga cikin bakwai na abubuwan ban mamaki a tarihi suka bace, Dunyar zamani a yau ta samar da wadanda suka maye gurbinsu. Domin kuwa kungiyar injiniyoyi ta kasar Amurka, wato “American Society of Civil Engineers” a Turance, ta samarwa da Duniya wadansu abubuwan ban mamakina zamani, wadanda suke a matsayin abubuwan bajinta da Injiniyoyin zamani suka yi a Karni na 20. Wadannan abubuwa sun hada da; Hanyar karkashin Kasa da aka gina daga kasar Faransa zuwa kasar Birtataniya, da doguwar Hasumiyar birnin Toronto wadda aka gina ta domin inganta harkar sadarwa, sai hamshakiyar Gadarnan ta Birnin San Francisco, ta hudunsu ita ce hayar Jirgin-ruwa ta Kasa da Kasa wadda aka haka a Kasar Panama, sai Madatsar-ruwa ta Itaipu, sai katafaren dogon gininan na birnin New York a Kasar Amurka wanda aka fi sani da suna “The Empire State Building’’a Turance, sai abu na 7 daga cikin abubuwan ban mamaki na zamani shine Ginin madatsun-ruwa na Kasar Holand ,wadanda aka fi sani da suna “The North Sea Protection works a Turance”

Idan kuma muka gangara ga abubuwan banmamaki na ikon Allah, anan sai muce Tsarki ya gabbata ga Allah gwani wajen Halitta. Saboda Idan mutum ya dubi wadannan abubuwa da zamu ambata a Kasa zai tabbatar da cewa akwai abinmamaki da kuma ban Al’ajabi a Tare da su, wadannan abubuwa dai sune; Wani rami na tsakanin tsaunuka mai haske a Kasar Spain da wani haske mai kamar hasken rana da ake gani da daddare a arewacin Duniya, Sai Dutse mafi girma a Duniya wato “Mount Everest” a Turance, sai dutse mai feshin wuta na kasar Mexico, sai babbar Matsayar Jiragen Teku da ke a Lardin Rio de Janero a Kasar Brazil, sai mafadar-ruwa ta Victoriya(Victoria Falls), Karshe da Wani wuri mai dutse a Teku wanda aka fi sani da suna “The great Barrier Reef” a Turance.

Wannan shine bayanan abubuwa bakwai akan nau’o’i daban-daban wadanda suka fi ban mamaki a Duniya.

Dafatan mai sauraron namu ya gamsu.