1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adamawa: 'Yan banga da dillancin makamai

Muntaqa Ahiwa/Kamaluddeen SaniMarch 11, 2016

Al'ummar jihar Adamawa da ke arewa maso gabashin Najeriya na bayyana fargaba su sakamakon kama wani dan banga da suka jagoranci fatattakar Boko Haram a jihar a baya, da laifin dillacin makamai a jihar.

https://p.dw.com/p/1IBwu
Nord Nigeria Anti Boko Haram Bürgerwehr Vigilante
'Yan banga da ke yaki da Boko Haram a AdamawaHoto: picture-alliance/dpa/Stringer

Ana dai zargin dan bangar ne da sayar da makaman ne ga 'yan fashi da kuma masu garkuwa da mutane gami da 'yan kungiyar Boko Haram ne a jihar.

Hakan dai ya fito fili lokacin wani samamen da fitaccen mafaraucin nan na arewacin Najeriya Ali Kwaraa ke yi a yankin kudancin jihar ta Adamawa, yankin da ke fuskantar radadin wata rigimar da aka zargi makiyaya da afkawa kabilar Bachama da haddasa asarar rayuka da kadarori a makwannin baya.

Bewaffnete Bewohner Patrouille Boko Haram Nigeria Chibok
'Yan banga da ke yaki da Boko Haram a AdamawaHoto: picture-alliance/AP Photo/S.Alamba

Kwamandan 'yan bangar da dubunsa ta cika, ya jingina hakan ne da neman kudin kula da motocin da gwamnati ta basu, da a cewarsa ke bukatar tayu da wasu kayayyaki, lamarin da jama'a da suka kafa alamar tambaya a kan haka.

Tuni dai wannan lamarin, ya fara daure kan jama'a da yanzu haka suke cikin farin cikin sakamakon samun zaman lumana a jihar da ta sha da kyar daga harkokin da suka shafi tabarbarewar tsaro.

Von Boko Haram zurückgelassener Panzer in Yola, Adamawa, Nigeria
Irin ta'adin da Boko Haram tayiHoto: picture alliance/AA/M. Elshamy

Jagoran da ya ja tawagar da ta kaiga kama wannan dan bangar da ake zargi da sayar da makamai, wato Alhaji Ali Kwaraa, ya ce wannan sakaci ne na mahukunta ga harkar tsaro, yana mai shawartar gwamnati ta tsaya ga tsaftace harkokin banga da ya ce akwai jabu a cikinsu.

La budda dai, akwai bukatar azamar mahukunta ganin yadda aka soma yada labaran da ke da hadari ga tsaro a jihar da har yanzu ta ke fama da hajijiyar tashie-tashen mayakan tarzomar Boko Haram.