1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adan ya katse hulɗa da kotunan Islama a Somalia

September 9, 2007
https://p.dw.com/p/BuBw
Wani attajirin dan kasar Somalia wanda ya tallafawa kawancen kotunan Islama da aka hambarar ya ce ya katse hulda da kungiyar bayan ya gana da FM Somalia Ali Mohammed Gedi a Djibouti. FM Gedi ya je Djibouti ne don ya nemi dan kasuwar Abubakar Omar Adan da yayi amfani da angizon sa wajen shawo kan sauran masu daukar makami na kotunan Islama da su amince da tayin gwamnati na yi musu afuwa. Adan ya fadawa manema labarai cewa ba shi ba kotunan Islaman. Gwamnatin wucin gadi ta FM Gedi na kokarin tabbatar da ikonta a Somalia wadda ta kasance cikin rudami tun baan da madugan yaki suka hamrad da tsohon dan kama karya Mohammed Siad Barre a shekarar 1991.