1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa da dokar canza kamannin gashin kai a Afirka ta Kudu

Zulaiha Abubakar/GATAugust 31, 2016

Dalibai a wata makarantar sakandare a garin Pretoria na Afirka ta Kudu sun yi zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu da wata doka da ta tanadi canzan kamannin gashin kansu.

https://p.dw.com/p/1Jt2i
Kenia Nairobi Perücken für Krebspatienten
Hoto: DW/A. Wasike

Dalibai a wata makarantar sakandare a garin Pretoria na Afirka ta Kudu sun yi zanga-zanga domin nuna rashin amincewarsu da wani mataki da makarantar ta dauka na komawa aiki da wata doka da aka gado tun daga turawan mulkin mallaka wacce ta tanadi tilasta wa dalibai bakar fata canza kamannnin gashin kansu ta yadda za ya yi laushi da sheki da yin magana da harshen Turanci, da kuma cin kwalliya da ado a makarantu. An jima ana muhawara a kan gashin kan 'yan Afirka wanda wasu suke yi wa kallon kazanta ne matukar ba a sauya masa kama ba da launi ta hanyar amfani da wasu sinadarai.

Yan'matan sun yi kira ga shugabar makarantar da sauran masu ruwa da tsaki a shugabancin makarantar da su dauki matakin gaggawa na canza wadannan dokoki. Wata tsohuwar dalibar makarantar ta ce magana da wani yare in ba turanci ba, kamar wulakanta kai ne ga abinda take cewa.

Afro-Amerikanisches Paar in den 70ern
Hoto: Getty Images/Hulton Archive

"Alal missali a lokacin taro ko a cikin aji duk bakaken dalibai za ka samu suna zaune guri daya sannan ba za su yi magana da yarensu ba don wannan babban kuskure ne, sai dai turanci"

Mata da yawa a Afirka sun rungumi kayan kwalliya masu canza launin gashin kai zuwa wata kala daban da kuma mikar da shi sabanin dunkulewa guri daya da aka san gashin matan Afirka da shi, kasancewa matan da suka canza launin gashin kansu ne abin kallo da misali, duk kuwa da cewar sinadaran da ake hada irin wadan kayan canza launin gashi suna shiga cikin jiki ta kofofin gashin kai tare da cutar da jiki. Mukwevo wata mata ce da take kishin gashin bakar fata ta ja hankali da cewa.

Africa on the Move Frauen Haare
Hoto: DW

"In na fahimce masu cewa a canza kammanin gashin kai, suna nufin in sayo wasu sinadarai in zuba wa kaina, wannan ba adalci ba ne, sun ci mutuncina a matsayina na mutum, haka aka haife ni, ban ga dalilin da zai sa in canza kamanni na ba sabi da ra'ayin wani, don kuwa wata alama ce da take nuna cewa ni baka ce"

To kamar yadda 'yan matan suke cigaba da zanga-zangar nuna adawarsu a kan barin bakin gashin kansu yadda yake da kuma yin magana da yarensu, haka batun nan na banbancin launin fata yake cigaba da ruruwa, wannan dai a iya cewa tuna baya ne na wani lokaci da ake hukunta 'yan kasar Afrika ta Kudu a kan magana da yarensu. Ministan Al'adu na kasar Nathi Mthethwa ya ce ba daidai ba ne a hana dalibai magana da harshensu na Afirka.