1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawa ta samu nakasu a siyasar Nijar

Mamane Kanta/YBAugust 15, 2016

Manyan jam'iyyun adawa a Nijar na kallon kallon tsakanin juna bayan da MNSD Nasara ta koma tafiya da masu mulki. Abin da wasu 'yan adawa ke cewa a yi dai mu gani.

https://p.dw.com/p/1JifR
Alhaji Saini Oumarou Oppositionspartei MNSD Nasara im Niger
Alhaji Saini Oumarou na jam'iyyar MNSDHoto: DW/M. Kanta

A Jamhuriyar Nijar canza shekar jam'iyar MNSD Nasara daga adawa zuwa gwamnati wani sabon babin siyasa kasar ce za'a shiga. Sai dai a bangaren hukumomin kasar ta Nijar da shugabannin jam'iyar PNDS Tarayya da ke rike da mulki sun yaba ma shugabannin jam'iyar MNSD Nasara wannan amuncewar tayin da suka yi musu.

Mohamed Bazoum ministan kula da harkokin cikin gida wanda shi ne shugaban jam'iyar PNDS Tarayya da ke mulki. Ya ce wannan mataki na babba cikin jam'iyyun adawa a Nijar ya yi kyau dan fiskantar kalubalen da kasar ke fiskanta:

"Yau shekara da shekaru kasar Mali na fama da matsalar tsaro abin da ke iya daukar lokaci dan haka dole a nemi hadin kai tsakanin manyan jam'iyyun adawa da masu mulki."

Ana dai zargin mahukuntan kasar da yawan ministoci ko mukaman siyasa da ake raba su a tsakanin mambobin jam'iyya mai mulki da ma na adawa , abin da a ke ganin zai karu da shigowar wannan jam'iyya ta adawa. Abin 'yan kasa ke kokawa ganin yanayi na tattalin arzikin kasar. Sai dai a fadar Bazoum ba haka lamarin yake ba.

Niger Wahlen Hama Amadou
Hama Amadou Modem Lumana AfirkaHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Mambobi a Modem Lumana Afirka ta Hama Amadou na ganin cewa komawar jam'iyyar ta MNSD Nasara bangaren gwamnati ba abu ne da zai karfafi adawa ba a kasar. Kuma idan ba su manta ba su ma sun shiga gwamnati a baya aka yi musu butulci.