1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawar Afirka na yunƙurin kama Al Bashir

July 14, 2010

Ƙungiyar gamayyar Afirka ta ce kama shugaban Al Bashir na Sudan da kotun duniya ke neman yi, bai zai magance matsalar da ake fiskanta a Darfur ba.

https://p.dw.com/p/OJIi
Shugaba Al Bashir na SudanHoto: DW/AP

Ƙungiyar gamayyar Afirka ta soki lamarin kotun hukunta manyan laifukan yaƙi na duniya na kama shugaban Sudan Umar Hasan Al Bashir ta ko halin ƙaƙa. Wannan ƙorafi ya zo ne kwanaki biyu bayan da kotun da cibiyarta ke birnin The hague ta fitar da sammace na biyu, na neman kama Al Bashir bisa zargin aikata kisan ƙare dangi watanni 16 da suka gabata. Sakataren zartaswa na Au wato Jean Ping, ya bayyana cewa tasa ƙeyar Al Bashir gidan yari, ba zai magance rikicin da ya gudana, tare da salwantar da rayukan ɗaruruwan mutane a yankin Darfur ba.

Galibin ƙasashen Afirka sun ƙi bayar da haɗin kan da kotu ke bukata domin cimma ma burinta. Maimakon haka ma sun gayyaci Al Bashir da aka zaɓa bisa tafarkin demokaradiya a kwanakin baya zuwa taron ƙolinsu da zai gudana a kampala na Uganda a ƙarshen wata. Mai shigar da ƙara a kotun, wato Luis Moreno Ocampo ya ce ina da ƙwararan shaidu da ke nuna cewa shugaban Al Bashir na da hannu dumu da dumu a ta'asar da ya salwantarar da rayukan mutane dubu 300, tare da da tilasa ma wasu ƙarin mutane kusan miliyon uku ƙaurace wa matsugunansu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Ahmed Tijjani Lawal