1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afganistan tana kokarin kwato birnin Kunduz a hannun Taliban

Kamaluddeen SaniSeptember 29, 2015

Shugaba Ashraf Ghani ya ce tuni dakarun kasar suka nufi Kunduz domin sake kwato birnin daga Taliban lamarin da ke faruwa lokacin da shugaban ke cika shekaru guda a kan karagar mulki.

https://p.dw.com/p/1GfTZ
Afghanistan Unabhängigkeitstag Präsident Ashraf Ghani
Hoto: Reuters/O. Sobhani

Dakarun kasar Afganistan da ke samun tallafin Amirka don yakar mayakan kungiyar Taliban na kokarin sake kwato birnin Kunduz da ke arewacin kasar bayan da 'yan Taliban sun kwace a karon faro tun lokacin da aka fatattake su shekaru goma 14 da suka gabata.

Sake kubcewar birnin a ranar Litinin da ta gabata daga dakarun kasar na kasancewa koma baya ga gwamnatin Shugaban Ashraf Ghani wacce ta cika shekaru guda a kan karagar mulki a wannan Talata.

Shugaban Ghani ya fada wa al'ummar kasar ta kafofin watsa labarai cewar tuni dakarun kasar suka isa Kunduz kana akwai karin wata bataliyar sojoji da ta rufa musu baya a kokarin da suke na sake kwato birnin bayan wani harin sama da sojojin Amirka suka kai a Kunduz domin taimakon sojojin Afganistan.