1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridu Jamus

March 15, 2009

Sharhunan Jaridun Jamus game da nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/HCSh
Tashe tashen hankula a MadagaskarHoto: picture-alliance/ dpa

Madagaskar/Somaliya

Jaridu da mujallun Jamus, a wannan makon sun gabatar da rahotanni masu yawan gaske akan al'amuran nahiyar Afurka. Amma maganar da ta fi ɗaukar hankali ita ce game da abin da jaridar Die Tageszeitung ta kira wani sabon salo na mulkin mallaka da wawason arziƙin da Allah Ya fuwace wa Afurka. Jaridar dai na batu ne game da yadda ƙasashen nahiyar ke sayar da manyan filayen noma ga ƙasashe na ƙetare a daidai wannan lokaci da ake fama da taɓarɓarewar tattalin arzikin duniya. Jaridar ta ci gaba da cewar:

Sayar da filayen Afirka:

"A sakamakon faɗuwar farashin mai da ƙarfe, da kuma koma bayan yawan masu zuba jari da yawon buɗe ido, kazalika da raguwar yawan kuɗaɗen da 'yan ci ranin Afurka ke aikawa zuwa gida, ƙasashen nahiyar, musamman ma masu arziƙi daga cikinsu suka fara sayar da filaye ga ƙasashen Asiya da na Larabawa don noma. Rahotannin da aka tara sun ce ƙasar Saudi Arabiya ta karɓi filin noma mai faɗin eka dubu 10 a wani yanki dake gaɓar kogin Nilu a ƙasar Sudan, akan tsabar kuɗi dala miliyan 95. Kazalika akwai rahotannin dake cewar ƙasar ta Sudan tuni ta yi wa ƙasashen Larabawa na yankin Golf alƙawarin ƙaddamar musu da filayen noma dake da faɗin eka dubu ɗari tara don amfani da su har tsawon shekaru 99. Kuma ko da yake an ƙorafi game da wannan sabon ci gaba mai kama da wani sabon salo na mamayar Afurka, amma akwai masu madalla da shi, inda aka ji Mary Fosi, ƙaramar minista a ma'aikatar kewayen ɗan-Adam ta ƙasar Kamaru tana mai nuna cewar wai Afurka na buƙatar masu zuba jari da zasu taimaka nahiyar ta samu ci gaba."

Marc Ravalomanana Präsident Madagaskar
Shugaban Madagaskar Marc RavalomananaHoto: AP

Madagaskar:

Wannan ci gaba dai na ɗaya daga cikin mafarin rigingimun da ake fuskanta a tsuburin Madagaskar, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, wadda ta ƙara da cewar:

"Tun abin da ya kama daga tsakiyar watan desamban da ya wuce ne ake fama da gwagwarmayar kama madafun iko tsakanin zaɓaɓɓen shugaba Marc Ravalomanana da kuma tsofon magajin garin Antananarivo Andry Rajoelina. Shi dai Rajoelina na zargin shugaba Ravalomanana da fatali da manufofin demoƙraɗiyya da kuma sayar da tsuburin gaba ɗaya ga ƙasashen ƙetare, dangane da shirin gwamnati na sayarwa da kasar Koriya ta Kudu fili mai faɗin eka miliyan ɗaya da dubu ɗari uku don noma masara da waken soja."

Somaliya:

Piraten in Somalia vor Gericht
´Yan fashin jirgin ruwa a SomaliyaHoto: AP

Ɗaya daga cikin abubuwan dake hana ruwa gudu wajen murƙushe matsalar fashe-fashen jiragen ruwa a tekun baharmaliya shi ne don turancin da akan fuskanta, kamar yadda aka gani dangane da wasu 'yan fashin da sojan ruwa na Jamus suka cafke baya-bayan nan, in ji jaridar Süddeutsche Zeitung. Jaridar ta ƙara da cewar:

"Wannan taɓargaza na mai yin nuni ne da yadda lamarin ke da sarƙaƙiya yake kuma hana ruwa gudu wajen haɗin kan ƙasashe don yaƙar matsalar fashin jiragen ruwa, kama dai daga haɗin kan sojojin har ya zuwa farautar 'yan fashin da gurfanar da su gaban kotu. A sakamakon haka waɗannan 'yan fashi zasu ci gaba da cin karensu ba babbaka, musamman ma kasancewar ba wani mai niyyar farautarsu a cikin ƙasar Somaliya, wadda yaƙi yayi kaca-kaca da ita."

Mawallafi: Tijani Lawal

Edita: Mohammad Awal