1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus (060204).

Mohammad Nasiru AwalFebruary 6, 2004
https://p.dw.com/p/BvqB
Jama´a barkan ku da warhaka. To bari mu fara da kasar Ivory Coast wato Kodivuwa, inda shugaban wannan kasa Laurent Gbagbo ya kai wata ziyara kasar Faransa da nufin gano hanyoyin dinke barakar da aka samu tsakanin gwamnatin birnin Paris da ta birnin Abidjan. A cikin dogon sharhin da ta rubuta jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta fara ne da cewa bisa ga dukkan alamu ziyarar da shugaba Laurent Gabgbo ya fara a ran alhamis a birnin Paris, zata taimaka wajen warware sabanin dake tsakanin gwamnatocin kasashen biyu. Jaridar ta ce bayan an shafe watanni 16 ana fama da yakin basasa sannan daga bisani aka cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya da Faransa ta jagoranci kullawa, amma bai yiwa gwamnatin shugaba Laurent Gbagbo dadi ba, wanda haka ya janyo zanga-zangar nuna kyama ga Faransa a birnin Abidjan, to yanzu haka dai kasashen biyu sun doshi hanyar maido da kyakkyawar huldar dangantaku tsakaninsu. Yayin wata gajeriyar ziyara da ya kai birnin Abidjan cikin makon jiya, ministan harkokin wajen Faransa de Villepin ya bayyana cewar kasar Ivory Coast na samun ci-gaba a kokarin samar da zaman lafiya a wannan kasa, inda ya kara da cewa shugaba Gbagbo na ba da muhimmanci ga rawar da Faransa ke takawa a cikin kasar. Jaridar ta ce gwamnatin Faransa dai ta gayyaci shugaba Gbagbo zuwa birnin Paris ne bayan da a cikin watan desamba, shugaban ya nuna shirin aiwatar dukkan ka´idojin yarjejeniyar samar da zaman lafiya musamman dangane da dokokin da suka shafi mallakar kasa da kuma zaben shugaban kasa da za´a gudanar cikin shekara ta 2005. Hakan dai zai ba tsohon FM Alassan Watara, wanda musulmi ne daga yankin arewacin kasar, tsayawa takara. Jaridar ta ce duk da cewa zaman lafiya ya fara wanzuwa a cikin kasar, bayan da dakarun gwamnati da na ´yan tawaye suka janye daga filin daga, kuma sojojin Faransa zasu ci-gaba da zama cikin kasar har shekara ta 2006 sannan kuma ministoci guda 9 daga bangaren ´yan tawaye sun koma bakin aikinsu, amma duk da haka da sauran rina a kaba, domin har yanzu kasar ba ta ga ko sisin kwabo ba daga cikin kudi dala miliyan 110 da take bukata don tafiyar da aikin kwance damarun mayakan kungiyoyin ´yan tawaye. Haka zalika har yanzu ana samun tashe tashen hankula tsakanin kungiyoyin da ba sa ga maciji da juna a yankunan da ke hannun ´yan tawaye. To Allah Ya sauwake. Yanzu kuma bari mu nufi kasar Angola, inda jaridar Tageszeitung ta rawaito wasu majiyoyin soji na cewa an fara wani gagarumin aiki da nufin kawo karshen hakan ma´adanan demond ba bisa ka´ida ba a yankin arewa maso gabashin wannan kasa. Yanzu haka dai akwai mutane kimanin dubu 290 ciki har da baki dubu 90 daga kasashe makwabta, musamman Kongo da ke wannan aiki mai hatsarin gaske a cikin kogin Kwanza. To sai dai tun ba´a kai ko-ina ba, wata kungiyar kare hakkin dan Adam a Kongo ta yi korafin cewa sojoji da ´yan sanda da jama´ar yankin na Kwanza na daukar matakan rashin imani akan bakin da ke zuwa wannan yanki yin ci-rani. Yanzu haka dai an fatattaki ´yan Kongo kimanin dubu 10 daga wannan yanki. Gwamnatin Angola dai ta ki ta tabbatar da hakan, sai dai ta ce an kama mutane 700 ciki har da baki 344, wadanda ke hakan demon ba bisa ka´i da ba.

A cikin wani rahoto da ta rubuta har wayau jaridar ta TAZ ta labarto wani mummunan hadarin jirgin ruwa da ya auku a cikin kogin Kongo a ran 25 ga watan janeru, amma sai bayan mako daya sannan wannan labari ya isa Kinshasa babban birnin JDK. Jaridar ta ce fasinjoji sama da 100 sun mutu a wannan hatsari sannan 200 sun bata. Jirgin ruwan dai ya dauko fasinjoji sama da 500, wanda hakan ya saba da yawan mutane da jirgin zai iya dauka. Jaridar ta ce wannan hadari dai ya auku ne a daidai lokacin da shugaba Joseph Kabila ya fara wani rangadin kasashen Turai ciki har da Jamus. A karshen wannan makon ne shugaba Kabila zai iso birnin Berlin, inda zai mika kokon bararsa ga mahukuntan wannan kasa.