1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

Mohammad Nasiru AwalMarch 2, 2007

Jaridun sun mayar da hankali a lardin Darfur, zaben shugaban kasar Senegal sai kuma a kasar Ghana.

https://p.dw.com/p/BvPL
Ministan cikin gidan Sudan, Ahmed Harun
Ministan cikin gidan Sudan, Ahmed HarunHoto: AP

A yau zamu fara ne da rahoton da jaridar FAZ ta buga game da sakamakon wani bincike da masu shigar da kara suka mikawawa alkalan kotun kasa da kasa dake birnin the Hague, wanda a ciki suka zargi manyan jami´an gwamnatin Sudan da hannu a kisan kiyashi da cin zarafin bil Adama da kuma yiwa mata fyade a lardin Darfur. Sakamakon binciken na mai shigar da kara Luis Moreno-Ocampo ya samu Ahmed Haroun tsohon karamin minista a ma´aikatar cikin gidan Sudan da Ali Kosheib madugun ´yan Janjaweed da laifin ba da umarnin keta hakkin Bil Adama da aikata laifukan yaki a shekara ta 2003 da ta 2004. Yanzu haka dai alkalan kotun na nazarin akan tuhumar kafin watakila su nema da a tura keyar mutanen biyu don su gurfana a gaban kotu ta kasa da kasa. To sai dai jaridar ta saka ayar tambaya game da sahihancin binciken musamman ganin cewa Moreno-Ocampo bai taba gudanar da wani bincike da kanshi a lardin Darfur ba. Ita ma jaridar TAZ ta tabo batun na tuhumar da aka aka yiwa babban jami´in gwamnatin na Sudan dsa kuma madugun ´yan Janjaweed. Jaridar ta ce yayin da kungiyoyin kare hakkin bil Adama ke korafin cewa wannan tuhumar ba ta wadatar ba, ita kuwa gwamnatin Sudan cewa ta yi an wuce gona da iri. Mai shigar da kara ya ce shaidar da ya tattara ta tabbatar da hannun mutane biyu a cikin aika-aikar da aka yiwa bakaken fatun lardin Darfur.

Yanzu kuma sai Senegal inda shugaban kasa Abdullah Wade ya sake lashe zaben da aka gudanar a ranar lahadi da ta gabata. A sharhin da ta rubuta jaridar Südd.-Z. cewa ta yi sakamakon farko ya nunar da cewa shugaban Wade mai shekaru 80 a duniya zai yi tazarce na tsawon sheakru 5 nan gaba akan karagar mulki. Jaridar kamar yadda aka saba ´yan adawa sun yi watsi da sakamakon zaben suna masu cewa an yi aringizon kuri´u. Tun gabanin zaben masu sukar lamirin sa sun ce shugaba Wade bai daukar matakan magance matsalar rashin aikin yi tsakanin matasa, wanda hakan ke tilasta musu yin kaura zuwa kasashen Turai. Ita ma jaridar FAZ ta rubuta sharhi game da sakamakon zaben tana mai cewa duk wani mai shekaru 80 a duniya dake daukar kansa a matsayin shugaba da zai tabuka wani abin kirkir to fa lalle shi wani dan siyasa ne mai da ke yin wani abin al´ajabi ko kuma masu kalubalantar sa ba su san inda aka dosa ba. To amma a dangane da shugaba Wade wanda ya lashe zaben Senegal a zagaye na farko, ba za´a iya ba da wani bayani cikin sauki ba.

A rahoton da ta rubuta jaridar FR ta ce kasar Ghana na da dukkan dalilai na gudanar da bukukuwan cikar ta shekaru 50 da samun ´yanci daga kasar Birtaniya, domin kasar na samun bunkasar tattalin arziki, tana da tsayayyar gwamnati ta demukiradiya yayin da ´yan kasar da ke ketare kuma ke komawa gida. Jaridar ta ce harkokin kasuwanci a kasar na habaka yayin da gwamnati ke aiwatar da manufofi na kare hakkin bil Adama da tabbatar da ´yancin ´yan jarida. Saboda haka ba abin mamaki ba ne da rukunin farko na kasar su kimanin miliyan biyu dake ketare suka fara komawa gida don ba da tasu gudunmawa don ci-gaban kasar wadda zata yi bukin cika shekaru 50 da samun ´yanci a ranar 6 ga wannan wata na maris.