1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A jaridun Jamus

Mohammad Nasiru AwalNovember 26, 2004

Halin rashin sanin tabbas a yankin gabashin kasar Jamhuriyar Demukiradiyyar Kongo shi ne abin da jaridun Jamus suka fi mayar da hankali a kai.

https://p.dw.com/p/Bvpd

To a wannan makon jaridun na Jamus sun fi mayar da hankali ne akan barazanar kai farmaki yankin gabashin JDK da shugaba Paul Kagamne na Rwanda ya yi. Sai kuma rikicin yaki ci yaki cinyewa a Darfur na yammacin Sudan.

A cikin sharhin da ta rubuta jaridar Frankfuter Allgemeine Zeitung (FAZ) ta rawaito shugaba Kagame ya na cewa kasarsa zata dauki matakan da suka da cewa akan ´yan tawayen Hutu dake gabashin kasar JDK, domin shirin MDD na kwance damarun mayakan Hutu da ake zargi da laifin yiwa dubun dubatan ´yan kabilar Tutsi kisan gilla a shekarar 1994, ya rushe. Shugaba Kagame ya bayyana kasancewar ´yan tawayen Hutu a gabashin Kongo da cewa tamkar an ma fara yaki ne.

Kimanin shekaru 10 bayan aukuwar kisan kiyashi a Rwanda, gwamnatin kasar ta tsananta kai farmaki akan ´yan tawayen Hutu dake gabashin Kongo, kuma yanzu haka ta yi barazanar kutsawa cikin yankin makwabciyarta wato Kongo, inji jaridar Tagesspiegel, a cikin sharhin da ta rubuta dangane da tabarbarewar halin da ake ciki a gabashin Kongo. To sai dai kwamitin sulhu na MDD, wanda ya girke da dakaru a yankin, yayi kira ga Rwanda ta ta girmama dokokin kasa da kasa na kare ´yancin jama´a. Jaridar ta rawaito majiyoyin MDD na cewa Rwanda ta tura sojoji dubu 3 zuwa Kongo.

Ita kuwa jaridar Tageszeitung (TAZ) cewa ta yi wannan barazana da Rwanda ta yi ta zo ne jim kadan bayan kammala taron wanzar da zaman lafiya da kasashen yankin gabashin Afirka suka yi a kasar Tanzaniya. A wajen taron kasashen sun amince da ka da su yiwa juna katsalanda a harkokin su na cikin gida kana kuma zasu taimaka wajen kwance damarun sojojin sa kai a wannan yanki.

Yanzu kuma sai Darfur inda har yanzu aka kasa gano bakin zaren warware rikicin da yaki ci yaki cinyewa a wannan yanki dake yammacin kasar Sudan. A ma halin da ake ciki MDD ta dakatar da aikin agaji da take yi a wannan yanki sakamakon sabon fada day a barke tsakanin dakarun gwamnati da na ´yan tawaye. A cikin wani rahoto da ta buga jaridar TAZ ta rawaito hukumar ba da taimakon abinci ta MDD na cewa ta dakatar da aiki a arewacin Darfur saboda sabon rikici da ya barke a wannan yanki, inda aka tsugunar da ´yan gudun hijira kimanin dubu 300. Yanzu haka dai ´yan gudun hijirar wannan yanki zasu kara tsunduma cikin wani mawuyacin hali. A dangane da batun wanzar da zaman lafiyar yankin na Darfur kuwa jaridar cewa ta yi samun nasarar shirin zaman lafiyar yankin zai dogara ne akan kwance damarun dukkan marikita a wannan yanki cikin lokaci guda, to amma kusan hakan ba zai yiwu ba, a wannan lokaci da muke ciki. Jaridar ta ce ko da yake zai yi wuya, amma dole ne a shigar da larabawa sojojin sa kai cikin shawarwarin samar da zaman lafiya, muddin a na son kwalliya ta biya kudin sabulu.

A game da kasar Ivory Coast wato Kodivuwa har wayau jaridar ta TAZ ta labarto mana cewar sojojin gwamnati na cewar dakarun Faransa sun janye daga wasu muhimman wurare da suka ja daga a birnin Abidjan, ciki har da filin saukar jirgin sama na birnin. An kai ga wannan matsayi ne sakamakon wata yarjejeniya da bangarorin biyu suka sanyawa hannu a karshen makon jiya. A kasar Uganda kuwa an fara samun alamun yin suklhu tsakanin gwamnati da ´yan tawayen kungiyar Lord´s Resistance Army. Yanzu haka dai ´yan tawayen sun shiga cikin shirin dakatar da yaki, da gwamnati ta sanar a farkon wannan mako, kana a lokaci daya kuma sun yi kira da a kara wa´adin wannan shiri daga mako daya zuwa kwanaki 100.