1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

December 4, 2007

Ethiopia Eritrea/ Taron AU da EU/ Rikicin Chadi

https://p.dw.com/p/CWLR
Meles Zenawi na ÄthiopiaHoto: AP Photo

Hauhawar tsamari tsakanin Ethiopia da Eritrea

Jama´a barkanku da warhaka. To a yau zamu fara ne da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda a cikin rahoton da ta rubuta mai taken hauhawar tsamari tsakanin Ehiopia da Eritrea ta fara ne da cewa wa´adin da kotun kasa da kasa ta bawa kasashen biyu na su amince da kan iyakokin su ya cika a ranar 27 ga watan nuwamba. Ta ce ana fuskantar barazanar barkewar sabon rikici tsakanin Ethiopia da Eritrea bayan yake yake kan iyaka sau biyu daga 1998 zuwa shekara ta 2000 da kasashen suka yi bayan kutse da dakarun Eritrea suka yi cikin Ethiopia. Mutane kimanin dubu 80 suka rasa rayukansu a rikicin a kwao karshensa albarkacin wata yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a birnin Aljiyas a shekara ta 2000. tun bayan da sojojin Ethiopia suka kutsa cikin Somalia, zaman doya da manja da ake yi tsakanin Ethiopia da Eritrea ya dauki sabon salo mai hadari, inda yanzu haka ake fargabar barkewar wani yakin kan iyaka tsakaninsu. Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung ta tabo batun rikicin inda ta rawaito masana harkokin yau da kullum na gargadi game da wani sabon yaki tsakanin kasashen na Ethiopia da Eritrea. Jaridar ta jiyo shugaban cibiyar nazarin kan rikice rikice na kasa da kasa wato ICG, Gareth Evans na cewa girke sojoji da tarin makamai a bangarorin kan iyakokin kasashen ya kai wani mizani mai ban tsoro wanda ka iya haddasa barkewar fada na ba da dadewa ba. Jaridar ta yi nuni da cewa duk wani yaki da zai sake barkewa to zai dagula al´amura a yankin kahon Afirka ga baki daya. Abin damuwa shi ne goyon bayan da wasu gwamnatocin kasashen yamma musamman shugaban Amirka George W Bush yake bawa Ethiopia wadda ke zaman kawar Washington a yakin da ta ke yi da ´yan ta´adda, wadanda ake zargi sun kafa sansanoni a kasashen Eritrea da Somalia.

Taron kolin kungiyar AU da kungiyar EU

Wani labarin na daban da har wayau jaridar ta Süddeutsche Zeitung rubuta ta ce za a gudanar da taron ƙoli tsakanin kungiyar tarayyar Turai EU da tarayyar Afirka AU ba tare da firaministan Birtaniya Gordon Brown ba, wanda ke ƙauracewa taron saboda shugaban Zimbabwe Robert Mugabe. Tun bayan da shugaba Mugabe ya ce zai halarci wannan taro, firaminista Brown ya ce shi kam zai yi zaman sa ne a gida. Tuni dai wasu majiyoyi musamman a nan Jamus ke cewa bai kamata a bari mutum guda ya yiwa manufofin EU a dangane da Afirka babakere ba. Su ma a nasu bangaren wasu ƙasashen Afirka sun yi barazanar ƙauracewa taron idan aka mayar da Mugabe saniyar ware. Jaridar ta ce da yake an bawa Mugabe goron gayyata to za a samu damar kulla yarjeniyoyi na bai daya a wannan taro wanda zai gudana a birnin Lisbon a ranar ga watan desamba.

Sabbin faɗace faɗace a Chadi

Yanzu bari mu garzaya ƙasar Chadi inda aka gwabza sabon fada bayan da ´yan tawaye suka ce sun kawo ƙarshen shirin tsagaita wuta. A wani rahoto da ta rubuta jaridar Neue Zürcher Zeitung cewa ta yi wata daya kacal bayan sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya wani mummunan fada ya barke tsakanin sojoji da ´yan tawaye a gabashin Chadi. Wannan gumurzu ya fi yin muni ne a kusa da sansanin ´yan gudun hijira na Farchana mai tazarar kilomita 100 gabas da birnin Abeche da ke kusa da kan iyaka da Sudan. Jaridar ta rawaito wata majiyar ´yan tawaye na cewa an kashe mutane da dama. An yi gwabza wannan fada wanda ke zaman mafi muni tun bayan watan afrilu a yankin da ake shirin girke wani bangare na sojojin kungiyar tarayyar Turai kimanin dubu uku da 500 ya zuwa ƙarshen wannan shekara don ba da kariya ga ´yan gudun hijira Darfur wadanda suke nemi mafa a wannan yanki, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ƙara da cewa faɗan na yankin kan iyaka na nuni da muhimmancin gaggauta tura dakarun na ƙungiyar EU.