1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

Lawal TijaniJuly 5, 2008

Sharhunan jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/EWyJ
Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe.Hoto: picture-alliance/ dpa


Zimbabwe/Mauritania

Ko da yake a wannan makon maganar Zimbabwe ce ta fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus ta la'akari da taron kolin shugabannin kasashen Kungiyar Tarayyar Afurka da aka gudanar a Sharm-El-Scheikh, amma fa jaridun kazalika ba su yi watsi da sauran sassa na nahiyar Afurka ba. Musamman ma halin da 'yan gudun hijira kan samu kansu a ciki a fafutukarsu ta neman wata kafa ta kyautata makomar rayuwarsu a nahiyar Turai. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Kasar Mauritaniya ta zama kyakkyawan misali a game da biya wa kasashen yammacin Turai bukatunsu na kare su daga 'yan gudun hijirar kasashen yammacin Afurka ko ta halin kaka. Kasar ta kan shiga kame-kame ba gaira ba dalili sannan ta tsare 'yan gudun hijirar a wata makaranta, wadda aka mayar da ita sansanin gwale-gwale. A saboda kasancewar wannan sansanin, wanda kasar Spain ta taimaka da makudan kudi domin sabunta gininsa a shekara ta 2006, ba ya da wani suna a hukumance ake kiransa sansanin gwale-gwale na Guantanamito. A baya ga wadannan fursinoni akwai kuma wasu 'yan gudun hijirar da suka tagayyara a wani yanki na yammacin Shara dake karkashin ikon Maroko, wanda aka bibbinne nakiyoyin karkashin kasa a cikinsa, wanda mazauna yankin ke kiransa wai Kandahar. Dukkan wadannan abubuwa na faruwa ne sakamakon matsin lamba daga Kungiyar Tarayyar Turai."

Ita ma jaridar Neues Deutschland tayi bitar matsalar 'yan gudun hijirar na Afurka, wadanda ta ce murnarsu kan koma ciki ne da zarar sun isa gabar tekun bahar-rum. Jaridar ta ci gaba da cewar:

"Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar su kan ratsa rabin fadin nahiyar Afurka a sayyada a kokarinsu na kaiwa zuwa tsuburan Ceuta da Melilla dake kasar Spain. Amma fa da zarar sun isa can sai murnarsu ta koma ciki, inda zasu samu kansu a sansanonin 'yan gudun hijirar dake fama da cunkoson mutane. Wannan maganar ta shafi 'yan gudun hijirar da za a iya cewar sun tsallake rijiya da baya ne, amma fa akwai wasu dubbannin da ba sa kai labari, inda alkaluma suka nuna cewar a shekarar da ta gabata 'yan gudun hijira dubu uku da dari biyar ne suka yi asarar rayukansu akan hanyarsu daga Afurka zuwa Spain."

Bisa ga dukkan alamu kasashen G8 da suka fi ci gaban masana'antu a duniya sun yi watsi da makomar Afurka, domin kuwa har yau ba su cika alkawarin da suka yi misalin shekaru uku da suka wuce ba na ribanya yawan taimakon da suke bai wa kasashen nahiyar nan da shekara ta 2010 domin su samu kafar yakar cututtuka irin su Aids, da kuma mummunan ummal'aba'isin nan da ake kira talauci. Bugu da kari kuma ana fuskantar barazana game da makomar shi kansa wannan alkawari, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito, inda ta ce akwai bayanan dake nuna cewar za a soke wannan alkawarin daga sanarwar bayan taron da ake da niyyar gabatarwa a taron kolin kasashen gamayyar ta G8 da za a gudanar a Japan mako mai zuwa. Idan har hakan ta faru murna zata koma ciki a game da fatan da aka yi na cewar zagayen tarukan na wadannan gaggan kasashen da suka fi ci gaban masana'antu a duniya zai taimaka a shawo kan matsalolin da ake fama da su a manufofin raya kasashe masu tasowa.