1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

Lawal, TijaniAugust 25, 2008

Sharhunan Jaridun Jamus akan Afirka

https://p.dw.com/p/F4Wh
Eagle Square AbujaHoto: DW


Daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a game da al'amuran Afurka a wannan makon shi ne yarjejeniyar da aka kulla akan hadin kan makamashi tsakanin Nijeriya da Jamus, wanda ka iya kasancewa wata ma'amalla irin salon ba ni gishiri in ba ka manda, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta nunar ta kuma kara da cewar:


"Ita dai Nijeriya tana bukatar taimako ne don kyautata harkokin samar da wutar lantarki, a madadin haka kasar ta yammacin Afurka ka iya sayarwa da kasashen Turai iskar gas. Wani abin lura da kuma kayatarwa game da wannan ci gaba shi ne, a baya ga kasancewar Nijeriya a matsayi na biyu a baya ga kasar Azerbaijan, da ta cimma irin wannan yarjejeniya ta bunkasa ma'amallar tattalin arziki, shugaba 'Yar Aduwa da kansa ne ya sa ido aka cimma wannan yarjejeniya".


Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung korafi tayi, tana mai sukan lamirin manufofin raya kasashe masu tasowa na Jamus, wanda ta ce ba su tsinana kome ba wajen yakar matsalar talauci. Jaridar ta ce lokaci yayi da za'a yi gyara ga wadannan manufofi, tun da an yi shekara da shekaru ana ba da taimakon kudi da tura dubban ma'aikatan raya kasa, amma ba a cimma nasara ba. Dalili kuwa shi ne mayar da hankali kacokam da aka yi wajen ma'amalla da gwamnatoci da kuma 'yan boko a maimakon talakawan kasa da lamarin ya shafa kai tsaye".


A wannan makon aka gudanar da taron kolin Afirka da kasar Turkiyya, wanda a baya ga wasu shuagabannin Afurkan ya kuma samu halarcin shugaba Omar Al-Bashir na kasar Sudan. Wannan dai shi ne karo na farko da shugaban ya kai ziyara wata kasa ta ketare bayan umarnin sammacensa da aka gabatar a kotun kasa da kasa akan miyagun laifuka. A lokacin da take sharhi game da makasudin wannan taro jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:


"Kasar Turkiyya dai tana fatan bunkasa huldar cinikinta ne da kasashen Afurka, wanda a shekara ta 2003 ya kama dala miliyan dubu biyar, kuma a bara ya kai dala miliyan dubu goma sha uku, zuwa dala miliyan dubu hamsin nan da shekara ta 2012. Hakan zai taimaka kasar ta Turkiyya ta cike gibin da take fama da shi sakamakon matsalolin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasashen Turai da na arewacin Amurka. Turkiyya dai a halin yanzu haka ita ce ta cikon 15 a jerin kasashen da suka fi samun bunkasar tattalin arziki a duniya".


A kasar Saliyo ana bukatar guraben aikin yi masu tarin yawa domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a wannan kasa da yakin basasa yayi kaca-kaca da ita a cewar jaridar Frankfurter Rundschau. Jaridar ta ce a yanzu haka kimanin kashi 80% na matasa a kasar ke zama hannu baka hannu kwarya, kuma basa hangen wata kyakkyawar makoma dangane da rayuwarsu. Tun bayan kawo karshen yakin basasar kasar ta Saliyo gwamnati ke famar sake gina tattalin arzikinta, amma tana fama da tafiyar hawainiya. Muddin ba tashi tsaye aka yi ba murna zata koma ciki dangane da zaman lafiyar kasar ta yammacin Afurka.