1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

Awal, MohammadNovember 7, 2008

A wannan makon bukin lashen zaɓen shugaban Amirka da Obama mai asali da Kenya ya fi ɗaukar hankalin jaridun.

https://p.dw.com/p/Fp70
Masu buki a Kenya game da lashe zaɓen Obama a AmirkaHoto: AP

A wannan makon mai ƙarewa jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni iri daban-daban akan halin da ake ciki a sassa daban-daban na nahiyar Afurka, musamman ma mawuyacin halin da aka sake faɗawa a ciki a Janhuriyar Demokraɗiyyar Kongo, sai bukukuwan da aka yi a sassa daban-daban a wannan nahiya sakamakon lashe zaɓen shugaban Amirka da Barack Obama mai asali da ƙasar Kenya ya yi. A rahotonta jaridar Süddeutsche Zeitung cewa ta yi:

"Mazauna a ƙauyen Kogelo inda kakar Obama ta ke sun bazu akan tituna suna kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe na farin ciki suna masu cewa za mu shiga fadar White House, muna son Obama. A ranar Laraba komai ya tsaya cak a ƙaramin ƙauyen dake yammacin ƙasar Kenya domin ɗansu wato Barack Obama ya lashe zaɓen shugaban Amirka. A duk faɗin ƙasar dai an yi ta bukukuwa inda shugaba Mwai Kibaki ya ayyana ranar 6 ga watan Nuwanba a matsayin ranar hutu ta ƙasa baki ɗaya don girmama Obama. Yanzu haka dai mazauna Kogelo na fatan nan ba da jimawa ba Obama zai kai ziyara a ƙauyen dake zama tushensa."

Ita kuwa jaridar Tageszeitung a rahotonta mai taken ilahirin ´yan Kenya sun yi bukin shugabansu, cewa ta yi "da sanyin safiyar ranar Laraba a faɗin ƙasar Kenya an bazu akan tituna don bukin shugaban Amirka baƙar fata na farko. A Kisumu hedkwatar lardin da mahaifin Obama ya fito farin cikin ba ya misaltuwa. A filin wasa na Jomo Kenyatta dubun dubatan mutane sanye da ƙananan riguna masu ɗauke da hoto da sunan Obama sun gudanar da bukukuwa kamar a ce ƙasar ta lashe kofin gasar cin ƙwallon ƙafa na duniya ne."

Yanzu sai ƙasar Janhuriyar Demoƙuraɗiyya Kongo. A sharhin da ta rubuta game da rikicin gabashin Kongo jaridar Berliner Zeitung ta yi tsokaci ne ga naɗin da aka yiwa tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo a matsayin wakili na musamman na babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon don kawo zaman lafiya a Kongo. Ta ce Obasanjo mai shekaru 71 zai yi murna ga wannan aikin da aka ba shi domin ya san dukkan waɗanda ke da hannu a rikicin. A lokacin da ya riƙe shugabancin ƙungiyar tarayyar Afirka a shekarar 2004, Obasanjo ya gaiyaci shugaban Kongo Josef Kabila da takwaran aikinsa na Rwanda Paul Kagame zuwa wani taron ƙoli. Wannan naɗin na matsayin ƙarfafa guiwa ga Obasanjo a wannan lokaci da yake fuskantar tuhume-tuhume na cin hanci da rashawa. Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung a rahotonta ta yi nuni da taron sasanta rikicin Kongo ne a birnin Nairobin Kenya inda ta rawaito Ban Ki Moon na cewa shi da kanshi zai yi shiga tsakani don samar da zaman lafiya a gabashin Kongo.