1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a Jaridun Jamus

Awal, MohammadNovember 15, 2008

Rikicin Kongo da tsamin dangantaka tsakanin Rwanda da Jamus suka fi ɗaukar hankalin jaridun.

https://p.dw.com/p/FvPL
Merkel da shugaban Rwanda Paul Kagame lokacin da dangantaka ke da kyauHoto: picture-alliance/ dpa

A wannan makon mai ƙarewa dai jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni akan abubuwan dake wakana a sassa daban daban na nahiyar Afirka. Amma da farko bari mu fara da tsamin dangantaka da ta kunno kai tsakanin Jamus da Rwanda sakamakon kame wata ´yar siyasar Rwanda da hukumomin Jamus suka yi.

A rahotonta jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce hulɗar diplomasiya ta shiga wani halin rashin sanin tabbas sakamakon wannan mataki da Jamus ta ɗauka na kame ´yar siyasar Rose Kabuye mai shekaru 47 bisa umarnin Faransa dake zargin jami´ar ta hannun damar shugaba Paul Kagame da hannu a kisan da aka yiwa tsohon shugaban Rwanda Juvenal Bruguiere. Ta ce hakan ya janyo jerin zanga-zanga yin tir a Rwanda bayan da gwamnatin ƙasar ta nuna rashin jin daɗinta wanda ya kai ga ta kira jakadanta daga Jamus zuwa gida sannan shi kuma jakadan Jamus a Rwanda ya bar ƙasar.

Kamun ´yar siyasar Rwanda ya haɗa kan ƙasashen Afirka wajen ƙalubalantar Turai, wannan dai shi ne taken rahoton jaridar Tageszeitung. Jaridar ta ce ba Rwanda kaɗai ta fusata da kame wannan jami´a tata ba, ita ma ƙungiyar tarayyar Afirka ba ta ji daɗin wannan mataki tana mai cewa barazana ce ga ƙoƙarin haɗin harkokin shari´a na ƙasa da ƙasa.

A game da rikicin gabashin Kongo kuwa har ila yau jaridar ta Tageszeitung cewa ta yi rikicin na yaɗuwa. Ta ce yayin da dakarun gwamnati ke tserewa daga ´yan tawayen Tutsi masu biyayya da Janar Laurent Nkunda bayan sun aikata ta´asa a wasu yankunan gabashin Kongo inda ´yan gudun hijira suke kwarara a ciki, Angola na matsa ƙaimi ne don taimakawa sojojin gwamnatin Kongo, yayin da a nata ɓangaren Rwanda ta tabbatar da cewa tsofaffin sojinta na marawa tawayen da Nkunda ke yi.

Har yanzu ba gwamnatin haɗin kan ƙasa a Zimbabwe, taken rahoton da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta rubuta kenan tana mai cewa jagoran ´yan adawa Morgan Changirai ya nuna adawa da shirin daidaitawa na ƙasashen kudancin Afirka. Ta ce shirin kafa gwamnatin haɗin kan ƙasa a Zimbabwe ya ci-tura bayan Changirai ya yi fatali da shawarar da wani taro na musamman da gamaiyar raya ƙasashen kudancin Afirka ya bayar na raba ikon kula da ma´aikatar cikin gidan Zimbabwe tsakanin ZANU-PF da MDC.

Nahiyar Afirka na cikin makoki na mutuwar mashahuriyar mawaƙiya kuma mai fafatukar ƙwato ´yancin baƙar fatar Afirka ta Kudu Miriam Makeba, inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Jaridar ta ce duniya ce gaba ɗaya ta yi rashin wannan gwarzuwa wadda da ake yiwa laƙabi da Mama Afirka. Ita ma jaridar Südddeutsche Zeitung ta rubuta dogon rahoton game da wannan gwarzuwar wadda ta yi amfani da hazaƙarta ta waƙa a matsayin wani makamin ƙwatar ´yancin baƙar fata. Jaridar ta ce zai yi wuya a samu wanda zai maye gurbin Miriam Makeba wadda ta kasance tamkar wata jakadiyar Afirka kuma babbar murya ga waɗanda ake keta haƙinsu.