1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A jaridun Jamus

February 21, 2009

Sharhunan Jaridun Jamus game da Afirka

https://p.dw.com/p/Gyfn
Shugaban JEM Dr. Khalil Ibrahim a tsakiya bayan tattaunawarsu da wakilan gwamnatin Sudan a QatarHoto: AP

Chadi/Sudan/Kenya

A wannan makon dai jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni masu tarin yawa akan al'amuran nahiyar Afurka. Amma da farko zamu fara ne da rahoton jaridar Frankfurter Allegeime Zeitung take cewar ko da yake a ranar 15 ga watan Maris mai kamawa ne aikin sojan kiyaye zaman lafiya na kasashen kungiyar tarayyar Turai da aka tsugunar a ƙasar Chadi zai kawo ƙarshensa, amma fa ga alamu za a ci gaba da tsugunar da wasu sojoji masu tarin yawa a harabar Chadin. Jaridar sai ta ci gaba da bayani akan maƙasudin tura sojojin zuwa wannan ƙasa, inda take cewar:

Chad

"An tura sojojin ne a matsayin gudummawar ƙasashen Turai a fafutukar shawo kan rikicin yankin Darfur da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa. Babban nauyin da ya rataya a wuyansu shi ne taimakawa wajen ba da kariya ga 'yan gudun hijirar Darfur dake tuttuɗawa zuwa gabacin Chadi da janhuriyar Afurka ta Tsakiya. Ƙungiyar ta tarayyar Turai dai tana tattare da imanin cewar wannan mazancin na shekara daya yayi nasara wajen tabbatar da tsaron lafiyar mutane sama da dubu 400, waɗanda suka koma lardinsu na Darfur".

Darfur/Sudan

Darfur UNAMID
Sojojin rundunar UNAMID a DarfurHoto: AP

A kuwa wannan makon aka samu wani kyakkyawan ci gaba inda 'yan tawayen Darfur da gwamnatin Sudan suka shiga tattaunawa da juna tare da samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin. Jaridar Die Tageszeitung ta gabatar da rahoto tare da saka ayar tambaya a game da ko ya-Allah za a samu wani sahihin zaman lafiya tsakanin shugaba El-Bashir da 'yan tawayen JEM. Jaridar ta ce:

"Shi dai shugaba El-Bashir har abada ba zai taɓa yafe wa JEM ba a game da yadda dakarunta suka kutsa kai har ya zuwa kurkusa da fadar mulki ta Khartoum shekarar da ta gabata. Ga alamu dai wannan yaƙin basasa na shekaru shida, wanda kuma ya halaka mutane sama da dubu 300 zai ci gaba. Domin kuwa a daidai lokacin da ake bikin rattaba hannu kan yarjejeniyarsu ta zaman lafiya a Qatar an sake fuskantar ɗauki ba daɗi tsakanin sojojin gwamnati da dakarun ƙungiyar tawaye ta JEM."

Kenya

Kibaki ernennt Odinga zum Premierminister
Shugaban Kenya Kibaki a dama da Firaminista Odinga, a haguHoto: AP

A can ƙasar Kenya har yau ana fama da tabon tashin-tashinar siyasar da ta biyo bayan zaɓen ƙasar da aka gudanar ƙarshen shekara ta 2007. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

"Akwai dalilai daban-daban a game da wannan tafiyar hawainiyar da ake fama da ita. A ɓangare guda akwai jami'an siyasar ƙasar dake hana ruwa gudu wajen kafa wata kotu da zata bi diddigin ta'asar saboda ba wa 'ya'yan jam'iyyarsu kariya, sannan a daya ɓangaren kuma akwai wadanda ba su yarda da alƙalan ƙasar ba suka kuma fi son ganin an kai maganar gaban kotun ƙasa da ƙasa. Kimanin mutane dubu ɗaya da dari uku suka halaka sannan wasu dubu 300 kuma suka yi asarar gidajensu sakamakon tashin-tashinar da ta biyo bayan zaɓen Kenya a watan Desamban shekara ta 2007.


Ahmad Lawal da Mohammad Awal