1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

Mohammad AwalMarch 9, 2009

Sharhunan Jaridun Jamus game da nahiyar Afirka

https://p.dw.com/p/H8Eq
Zanga-zangar nuna goyon baya ga shugaban Sudan Al-BashirHoto: AP

Sudan ICC/Gini Bissau/Zambiya

Babban abin da ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon dai shi ne hukuncin da kotun ƙasa-da-ƙasa akan miyagun laifuka dake birnin The Hague na ƙasar Netherlands ya zartar na cafke shugaban ƙasar Sudan Umar Al-Bashir. Da farko zamu fara da sharhin jaridar Süddeutsche Zeitung dake cewar:

Sudan ICC

Omar Hassan Ahmad al-Bashir Präsident Sudan
Shugaban Sudan Omar Hassan Ahmad al-BashirHoto: picture-alliance/ dpa

"Ko da yake alƙalan kotun ƙasa-da-ƙasa dake birnin The Hague sun taka rawar gani wajen cika sharuɗɗan kotun, amma fa da yawa daga al'umar Afurka na tattare da ra'ayin cewar kotun dai an kafa ta ne don shari'ar 'yan ƙasashe masu tasowa. Kuma ko da yake a wasu batutuwan da dama su kansu ƙasashen Afurka ne suka nemi sa bakin kotun, amma dangane da Sudan kwamitin sulhu na MDD ne ya bai wa kotun damar yin haka tare da amincewar Amurka, wadda a haƙiƙa bata yi amanna da kotun mai shari'ar miyagun laifuka na yaƙi ba."

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung a cikin nata sharhin nuni tayi da cewar:

"A haƙiƙa alƙalai a kotun ƙasa-da-ƙasa akan miyagun laifukan yaƙi ba su da wani zaɓi, domin kuwa da a ce sun ƙi su ba da umarnin cafke shugaba Umar Al-Bashir da kuwa hakan ya zama tamkar wani lasin ga masu cin karensu babu babbaka a lardin Darfur. Amma giɓi ɗaya dake tattare da hukuncin shi ne kasancewar bata haɗa da zargin kisan kiyashi ba, wanda ke ɗaya daga cikin laifuffukan da mai ɗaukaka ƙara Luis Moreno-Ocampo ya gabatar akan shugaba Al-Bashir. Ƙasar Sudan gaba ɗayanta na bukatar sabuwar alƙiblar siyasa, muddin hakan ta samu to gurfanar da Bashir a gaban kotun ba zai ta'azzara ba."

Guinea Bissau Soldaten
Sojoji a Gini-BissauHoto: AP

Gini Biassau

An sake fuskantar rikici a ƙasar Guinea-Bissau, inda sojoji suka kashe shugaban ƙasa don ramuwar gayya akan kisan da aka yi wa hafsan hafsoshinsu, kamar yadda jaridar Neues Deutschland ta rawaito ta kuma ci gaba da cewar:

"Gaba mai tsananin gaske dake akwai tsakanin Shugaba Viera da hafsanhafsoshin sojansa Batista Tagme Na Wai ba ɓoyayya ba ce a mitsitsiyar ƙasar Guinea-Bissau dake yammacin Afurka. An dade mutane na gunagunin cewar ko Ya-Alla daga cikinsu wa zai fara kashe ɗan-uwansa. Dukkansu biyu sai da suka tsallake rijiya da baya a yunƙure-yanƙure na kisan gilla a makonnin da suka wuce, inda suka ɗora wa juna laifi. A yanzu dai dukkansu biyu sun mutu, kuma ba wanda ya san tahaƙiƙanin wanda zai mulki ƙasar mai fama da rikici da juye-juyen mulki nan gaba."

Zambiya

Ƙsashe da dama na Afurka na ci gaba da fama da raɗaɗin matsalar kuɗin da ta samu a kasuwannin duniya. A lokacin da take gabatar da rahoto akan haka jaridar Berliner Zeitung ta ba da misali da ƙasar Zambiya. Jaridar ta ce:


"A misalin shekara ɗaya da ta wuce kome na tafiya salin-alin dangane da ƙasar Zambiya, wadda take tinƙaho da bunƙasar kashi shida cikin ɗari ga tattalin arziƙinta da kuma koma bayan hauhawar farashin kaya. Amma a cikin ƙiftawa da Bisimilla Zambiya ta samu kanta cikin mawuyacin hali sakamakon faɗuwar farashin jan ƙarfe da sauran albatrkatun ƙasar dake samar mata da kuɗaɗen shiga. Ba Zambiya kaɗai ba, akwai ƙasashe da dama na nahiyar Afurka da suka shiga irin wannan mawuyacin hali sakamakon koma bayan bukatar ɗanyun kayayyaki a kasuwannin duniya."