1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Afirka ta Tsakiya ya yi kwanaki 100

Abdul-raheem HassanJuly 11, 2016

Shugaban kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera ya gudanar da bikin cika kwanaki 100i da hawa kan karagar mulkin kasar, to amma har yanzu tsugune bata kare ba.

https://p.dw.com/p/1JNEr
Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin Archange Touadera
Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin Archange TouaderaHoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

Shugaba Touadera dai ya bayyana cewa har yanzu kasar na cikin tsaka mai wuya ta fuskar rashin tsaro. Shugaba Touadera ya fara aiki ne a watan Maris din shekara ta 2016 da nufin maido da martabar sojojin kasar da raba 'yan ta'adda da makamai, wanda hakan zai bai wa 'yan kasar kusan 3000 da ke gudun hijira a kasar Kamaru damar komawa kasarsu ta haihuwa. Da ya ke jawabi a bikin cika kwanaki 100 a kan karagar mulkin, shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar yayi karin haske kan binciken da suke gudanarawa a kan gwamnatin da ta shude.

Ya ce: "Ba wai muna binciken gwamnatin da ta gabata da wani nufi ba, amma ya na da kyau a san aikin da gwamnatin baya suka kaddamar. Ta haka ne za'a iya gyara kuraran da aka yi."