1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afka wa baƙi a ƙasar Belgium na ta ƙara haɓaka.

YAHAYA AHMEDMay 12, 2006

A ran alhamis ne wani ɗan tsagera na ƙasar Belgium ya bindige wata mace baƙar fata da ɗanta mai jini biyu a birnin Antwerpen, sa'annan ya ji wa wata mace baturkiya kuma rauni.

https://p.dw.com/p/BvTc
Injunan ɗaukan kaya a tashar jirgin ruwan Antwerpen na ƙasar Belgium.
Injunan ɗaukan kaya a tashar jirgin ruwan Antwerpen na ƙasar Belgium.Hoto: AP

Magajin garin birnin Antwerpen Patrick Janssens, na cikin waɗanda suka yi kakkausar suka ga ɗanyen aikin da wani matashi mai shekaru 18, ɗan wata ƙungiyar ’yan tsageru, ya gudanar a birnin jiya. Kamar yadda ya bayyanar:-

„Labarin abin da ya auku ya gigitad da ni. Har ila yau ina mamakin yadda, wani zai iya tashi da rana tsaka, ya shiga shago ya sayi makami, sa’annan ya fito, ya dinga buɗe wa mutane wuta, waɗanda ya zaɓe su musamman saboda bambancin launin fatarsu da nasa. Wannan dai ɗanyen aiki ne da bai kamata mu amince da shi ba.“

Kamar dai magajin garin na Antwerpen, haka ma jama’a da dama na ƙasar Belgium suka nuna ɓacin ransu. Kowa dai na mamakin yadda wannan lamarin ya auku. Haka kawai ba zato ba tsammani, sai wani matashi ya shiga gari da tsakar rana, ɗauke mashingan, ya yi ta ɗirka wa mutane darma. Shi dai wannan matashin ya fara buɗe wa wata baturkiya ne wuta, wadda take zaune a kan wani benci tana karanta jarida. Matar ta ji munin rauni, kuma a halin yanzu tana kwance ne a asibiti, rai hannun Allah. Kamar wannan bai wadatar ba, sai matashin, wani ɗan gungun ’yan tsageru, mai shekaru 18 da haihuwa, ya yi gaba kuma. Da ya ga wata mace mai baƙar fata, wadda ke kulawa da ɗan yaro mai jini biyu, kawai sai ya buɗe musu wuta. Nan take ya halakad da su. Wani ɗan sanda da Allah ya sa yana kusa da gun ne ya kawo ƙarshen wannan annobar, yayin da shi ma ya buɗe wa matashin wuta, bayan ya ƙi bin umarninsa ya miƙa wuya. A halin yanzu dai, matashin ma na kwannce a asibiti. Jami’an tsaro sun ce saboda raunin da ya ji da kuma halin da yake ciki, ba a iya an yi masa tambayoyi ba. Har ila yau dai, ana nan ana ta raɗe-raɗi, kan musabbabin wannan ɗanyen aikin. Irin askin da matashin ya yi da kuma alamun jarfan da ke jikinsa, na nuna cewa daga da’irar ’yan tsageru masu tsatsaurar ra’ayi yake.

Firamiyar ƙasar Belgium ɗin, Guy Verhofstadt, wanda shi ma ya ce ya gigita da jin labarin wannan ɗanyen aikin, ya bayyana cewa:-

„Wannan ɗanyen aiki ne na masu matuƙar nuna wariyar al’umma. Yanzu dai lokaci ya zo da ya kamata ko wane ɗan ƙasar nan, ya farga, ya kuma fahimci inda aƙidar tsatsaurar ra’ayi ta mai da alƙibla.“

Birnin na Antwerpen, mai tsahar jirgin ruwa, da ma can sananne ne da kasancewa cibiyar jam’iyyar ’yan tsagerun nan ta „Flamms Belang“. A zaɓen ƙananan hukuumomin da aka yi a kawanakin baya, jam’iyyar ta sami kashi ɗaya bisa uku na ƙuri’un da aka ka da. A lokuta da dama dai, a kan sami ɓarkewar tarzoma, a birnin, mai ɗimbin yawan mazauna baƙi. Mahukuntan ƙasar na fargabar ɓarkewar wata tarzoman kuma. Sabili da haka ne dai Firamiya Verhofstadt, ya yi kira ga jama’a da su kwantad da hankalinsu, da bayyana cewa:-

„Dole ne mu ɗau duk matakan hana duk abin da zai tsunduma al’ummanmu cikin wani jerin tashe-tashen hankulla da nuna ƙyama. Al’umman wannan ƙasar dai tun da ma can masu sauƙin kai ne – kuma haka ya kamata mu ci gaba da kasancewa.“

A makon da ya gabata ma, sai da ’yan tsageru suka afka wa wani bafaranshe mai baƙar fata da abokinsa ɗan ƙasar Belgium ɗin, a garin Brügge, inda suka ji musu munanan raunuka. A ƙarshen wannan makon ne ma aka shirya gudanad da wata zanga-zanga a garin don nuna ɓacin rai da adawa ga wariyar al’umma da kuma ƙyamar baƙi.