1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun

Lawal, TijaniOctober 13, 2008

A wannan makon jaridun sun fi mayar da hankali ne kan matsalar kwararowar baƙi daga Afirka zuwa Turai.

https://p.dw.com/p/FYYT
Kwararar bakin haure zuwa Turai babu kakkautawaHoto: picture-alliance/ dpa

To daga cikin muhimman batutuwan da suka fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus akan al'amuran Afurka a wannan makon har da sabon ci gaban da ake samu na yunƙurin tuttuɗowar 'yan gudun hijirar Afurka zuwa nahiyar Turai, inda a wannan makon aka buɗe cibiyar Ƙungiyar Tarayyar Turai akan 'yan gudun hijira a Bamako ta ƙasar Mali. Amma da farko zamu fara ne da duba matsalar 'yan gudun hijirar daga nahiyar Afurka, inda a wannan makon aka samu wasu da suka sauka a tsuburin Lampedusa na ƙasar Italiya. Jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta rahoto akan haka tana mai cewar:

"A haƙiƙa a taswirance tsuburin Lampedusa wani ɓangare ne na nahiyar Afurka, saboda ya fi kusa da nahiyar akan tsuburin Sisiliya a ƙasar Italiya. Ta la'akari da haka bai zama abin mamaki ba kasancewar tsuburin na ɗaukar hankalin 'yan gudun hijirar Afurka dake fafutukar shigowa Turai, inda a wannan makon sai da jami'an tsaron tekun Italiya suka tsamo wasu 'yan gudun hijirar dake cikin hali na ƙaƙa-nika-yi a tekun bahar-rum."

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta yi bitar matsalar inda take cewar:

"A cikin sa'o'i 24 kacal, 'yan gudun hijirar Afurka dubu ɗaya suka sauka tsuburin Lampedusa a cikin wasu kwalekwale guda 12 daga ƙasar Libiya, lamarin da ya sanya jami'an tsaron Italiya ke zargin Libiyan da rashin cika alƙawarin da tayi na hana 'yan gudun hijirar amfani da harabarta don shigowa nahiyar Turai. To sai dai kuma ƙungiyar Kula da 'yan gudun hijira ta ƙasa da ƙasa tayi marhabin da take take-taken Libiyan, wanda bisa ga alamu tayi wa maganar riƙon sakainar kashi ne saboda rashin cika alƙawarin da ƙasashen Turai suka yi mata na taimako."

A fafutukar tinkarar wannan matsala a wannan makon ƙuniyar Tarayyar Turai ta buɗe wata cibiya ta 'yan gudun hijirar a Bamako ta ƙasar Mali, inda take fatan wayar da kan matasa a game da kykkyawar damar da suke da ita na kyautata makomar rayuwarsu a gida da kuma irte-iren wahalar da zasu fuskanta in sun shigo nahiyar Turai. Cibiyar ta tanadar da matakai na koyar da sana'o'in hannu ga waɗannan matasa akan manufa in ji jaridar Der Tagespiegel.

Jaridar ta Der Tagesspiegel har ila yau ta leƙa ƙasar Zimbabwe, inda murna ke neman komawa ciki makonni uku kacal bayan cimma daidaituwa akan kafa wata gwamnati ta haɗin kan ƙasa. Jaridar ta ce:

"Ko da yake dukkan ɓangarorin da lamarin ya shafa suna da rabonsu na alhakin wannan sabon ci gaba, inda MDC ta 'yan hamayyxa ta dage akan lalle sai an ba ta muhimman ma'aikatun gwamnati, sannan shi kuma Mugabe ke ƙoƙarin yin amfani da mawuyacin halin da ake ciki a kasuwannin hada-hadar kuɗi na duniya domin ganin yarjejeniyar ta su ba ta samu shiga ba, amma babban ummal'aba'isin matsalar shi ne kakka be shugaba Mbeki da aka yi daga karagar mulkin Afurka ta Kudu, wanda shi ne ainifin mutumin da yayi jagora ga ita muwafaƙar da aka cimma."