1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afruka A Jaridun Jamus

March 11, 2005

A wannan makon jaridun Jamus su gabatar da rahotanni iya gwargwado akan al'amuran Afurka tare da mayar da hankali ga kasar Saliyo

https://p.dw.com/p/BvpP

A wannan makon mai karewa jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al’amuran nahiyar Afurka, abin da ya hada har da halin da ake ciki a Saliyo dangane da shari’ar masu laifukan ta’asar yakin basasar kasar tsakanin 1991 zuwa shekara ta 2001. A lokacin da take gabatar da rahoto akan wannan shari’a jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG mai ra’ayi irin na mazan jiya cewa tayi:

"A wannan makon ne ake gabatar da matakin karshe na shari’ar mutanen da ake zarginsu da laifukan keta haddin dan-Adam da cin mutuncin mata da tilasta aikin sojan yara kanana a yakin basasar kasar Saliyo na tsawon shekaru goma. A cikin watanni goma sha biyun da suka wuce an gurfanar da mutane 13 a gaban kotun kasa da kasa dake ma’amalla ta kut-da-kut da MDD domin amsa laifukan datse gabobin mutanen da ba su san hawa ba ba su san sauka ba a yakin basasar. Wannan maganar ta shafi shuagabannin ‘yan tawaye na RUF da kungiyoyin tsaron kai na Kamajor. Kimanin mutane dubu 200 suka yi asarar rayukansu a yakin basasar kasar ta yammacin Afurka daga 1991 zuwa shekara ta 2001."

A wannan makon ministan harkokin wajen kasar Ruwanda Charles Murigande yayi kiran katsalandan sojojin kasa da kasa a gabacin Kongo domin karya alkadarin ‘yan Hutu dake amfani da harabar kasar domin shirya hare-harensu na sare-ka-noke a Ruwanda. A cikin wata hira da jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi da ministan harkokin wajen na Ruwanda, yayi nuni da cewar:

"A lokacin da Ruwanda ta tura sojojinta zuwa yankin gabacin Kongo an samu kafar gurgunta matsayin ‘yan sare-ka-noken. Kuma ba don amincewar da kasar tayi da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka rattaba hannu kanta a Lusakan Zambiya a shekara ta 1999 ba da kuwa a yanzun babu shauran ko da kwaya daya na ‘yan tawayen Hutun a wannan yanki. Ministan harkokin wajen na Ruwanda dai yana zargin gwamnatin shugaba Joseph Kabila da laifin ruwa wa ‘yan tawayen baya."

Akwai alamun shiga takun-saka tsakanin Zimbabwe da Afurka ta Kudu sakamakon ikirarin afuwar da shugaba Mugabe yayi ga wasu sojan haya ‘yan kasar ATKn su 62, wadanda aka ce suna kan hanyar komawa gida, amma har ya zuwa yanzun ba a ji doriyarsu ba, kamar yadda jaridar NEUES DEUTSCHLAND ta nunar ta kuma ci gaba da cewar:

"Bayan ikirarin afuwar da aka yi ga sojan hayar ATK su 62 dake tsare a kasar zimbabwe, rahotanni sun ce an sake tasa keyar fursinonin zuwa gidan kurkuku, wai saboda lauyan gwamnati ya ce matakin na afuwa ya saba da tsarin dokokin kasar Zimbabwe. Jama’a a ATK na tattare da ra’ayin cewar wannan ikirari wani mataki ne na yaudara kawai, saboda babu wata kotu a kasar Zimbabwe da ta isa ta dakatar da zartaswar shugaba Mugabe. Bugu da kari kuma wannan babban kaye ne ga shugaba Mbeki, wanda bai dadara ba yana mai neman bakin zaren warware rikicin kasar Zimbabwe a siyasance. Amma a daya bangaren manazarta na ganin wannan ci gaba wata alama ce ta sabanin dake akwai tsakanin su kansu wakilan jam’iyyar ZANU-PF dake mulki, a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaben kasar Zimbabwe a ranar 31 ga watan maris."