1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka a Jaridu

Lawal, TijaniFebruary 8, 2008

Sharhunan Jaridun Jamus kan Afurka

https://p.dw.com/p/D4hB
Tsohon Babban Sakataren MajalisarƊunkin Ɗuniya , Kofi Annan.Hoto: AP


Zimbabwe/Tchad/Kenya


Zimbabwe

A wannan makon dai halin da ake ciki a kasar Chadi shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus, ko da yake da farko zamu fara ne da duba matsin kaimi ne da shugaba Mugabe ke fama da shi ne a cikin gida dangane da rarrabuwa a jam'iyyar Zanu-Pf mai mulki jim kadan kafin zaben shugaban kasar da za a gudanar watan maris mai zuwa. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Jam'iyyar gwamnatin Zimbabwe ta Zanu-Pf bata da kwanciyar hankali yanzu haka tun bayan da wani tsofon mukarrabin shugaba Robert Mugabe yayi masa huruji jim kadan kafin zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa ranar 29 ga watan maris. Tsofon ministan kudi Simba Makoni, wanda aka kakkabe shi daga mukaminsa a shekara ta 2002, ya shigar da siyasar Zimbabwe cikin wani sabon yanayi bayan da ya fito fili ya bayyana shirinsa na shiga takarar neman zama shugaban kasa. Ba kuwa shi kadai ne ya dawo daga rakiyar Mugabe ba, akwai 'ya'yan jam'iyyar ta Zanu-Pf da dama da suka dawo daga rakiyar salon kamun ludayin Mugabe, lamarin da ya sanya akasarin al'umar Zimbabwe ke fatan samun canji a zaben na watan maris."

Tchad

Dangane da halin da ake ciki a kasar Chadi kuwa jaridar Die Zeit tayi nuni ne da rawar da Faransa ke takawa a kasar Chadi bayan ta kwatanta shugaba Idris Deby a matsayin dan gaban goshin shugaba Sarkozy. Jaridar ta ce:


"Bayan shekaru 48 da samun 'yancin kai, kasar Chadi har ila yau, ita ce dandalin soja mafi muhimmanci ga kasar Faransa a nahiyar Afurka kuma take-takenta a game da kasar mai arzikin mai da uranium daidai yake da zamanin mulkin mallaka. Idan ba a manta ba a shekara ta 2006 kasar ta Faransa sai da ta taimaka wajen hana kifar da mulkin dan kama karya Idris Deby, mai yi mata biyayya sau da kafa. Kuma tun baya da 'yan tawaye suka fara bude wuta akan kasaitacciyar fadarsa dake N'djamena, shugaban ke tuntubar uban-gidansa Nikolas Sarkozy, ta wayar tarfo a kowace rana. Ta la'akari da haka bai zama abin mamaki ba ganin yadda Faransa ta tashi gadan-gadan domin rufa wa dan kama karyar baya."


Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

"Yawa-yawanci akan danganta rikicin Chadi da yakin basasar Sudan a lardin Darfur, alhali kuwa a hakikanin gaskiya ainifin rikicin Chadin, wanda aka yi sama da shekaru 20 ana fama da shi, shi ne ummal'aba'isin mawuyacin halin da ake ciki a lardin na yammacin kasar Sudan. Da yawa daga larabawan janjaweed 'yan usulin Chadi ne daidai da da yawa daga cikin 'yan tawayen dake fafatawa da su. Mawuyacin halin da shiga a Chadi a yanzun yana mai yin nuni ne da yadda gwagwarmayar yada madafun iko ta kai kololuwarta a wannan yanki."


Kenya

Kasar Afurka ta Kudu ta fallasa wata mummunar tabargaza dangane da yunkurin sasanta rikicin kasar Kenya da tsofon sakataren Majalisar Dunkin Duniya Kofi Annan yake yi, kamar yadda jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rawaito, inda ta ce hukumar leken asirin kasar ta Kenya na bin diddigin shawarwarin Kofi Annan a asurce. Ta kuma kara da cewar:


"An dai shiga takun saka tsakanin Kenya da Afurka ta Kudu, tun bayan da kasar ta Kenya ta ce fau-fau ba zata amince a nada Cyril Ramaposa, dan kasar Afurka ta Kudun ya jagoranci shawarwarin sasanta rikicin da ya barke tsakanin gwamnati da 'yan hamayya sakamakon zaben watan desamban da ya gabata ba. Babu dai wata alama ta ci gaba a yunkurin sasantawar na tsofon sakatare-janar Kofi Annan, kuma tuni Amurka ba da sanarwar dakatar da ba da izinin shiga kasar ga jami'an siyasar Kenya da suka hada da na gwamnati da kuma 'yan hamayya."


A nata ra'ayin jaridar Rheinischer Merkur cewa tayi duk mai fatan shawo kan matsalar zub da jinin da ake fama da ita a kasar Kenya yanzu haka, to wajibi ne yayi gyara ga salon rabon filaye a kasar. Domin kuwa bayan samun 'yancin kanta daga turawan Birtaniya a karkashin Jomo Kenyatta, dan kabilar Kikuyu, aka fara raba wa 'ya'yan kabilar raba fiyalen noma mai albarka a yankin arewa-maso-yammaci, wanda yanki ne na 'yan kabilun Kalenyin da Luo da kuma Massai. Muddin ba tinkarar wannan matsala aka yi daga tushenta ba, ba za a iya dinke barakar da ta biyo bayan zaben watan desamba a kasar ta Kenya ba."