1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

June 1, 2007

Bikin rantsar da sabon shugaban Nijeria shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BtvS

A wannan makon jaridun Jamus sun fi mayar da hankalinsu ne akan bikin rantsar da sabon shugaban Nijeriya Alhaji Umaru Musa ‘yar Adua da kuma alkawarin da yayi na tinkarar matsalolin dake addabar kasar da kuma yin bakin kokarinsa wajen shawo kan rikicin Nigerdelta. A cikin nata rahoton jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:

“A karkashin wani yanayi na gagarumar adawa, amma ba tare da wani tashin hankali ba aka gabatar da bikin rantsar da sabon shugaban kasar Nijeriya Umaru Musa ‘Yar Adua, inda ya maye gurbin tsofon shugaba Olusegun Obasanjo bayan wa’adin mulki har sau biyu. Wannan dai shi ne karo na farko da wani zababben shugaba na farar fula da mika ragamar mulki ga wani zababben shugaban a tarihin Nijeriya. A cikin jawabinsa dai sabon shugaba ya ce zai ba da fifiko ne ga matakan shawo kan rikicin yankin Nigerdelta dake gurgunta tattalin arzikin Nijeriya. Mai yiwuwa ya samu nasara ganin cewar a karo na farko an nada wani mataimakin shugaban kasa daga yankin na Delta.”

Ita kuwa jaridar General Anzeiger cewa tayi:

“An dai rantsar da sabon shugaba a Nijeriya a karkashin tsauraran matakai na tsaro domin hana zanga-zangar ‘yan adawa dake korafin magudi a zaben kasar da aka gudanar watan afrilun da ya wuce. Amma a baya ga zargin magudi, wani abin da ‘yan adawar ke Allah Waddai da shi kuma shi ne kasancewar tsofon shugaba Olusegun Obasanjo, wanda shi ne ainifin wanda ya zabi Umaru Musa ‘Yar Adua domin ya maye gurbinsa, jim kadan kafin mika sandan mulkin bai yi wata-wata ba wajen mukarrabansa ne suka ci gaba da rike muhimman mukamai a kamfanonin gwamnati, kamar dai babbar matatar mai ta kasar tare da mayar da kamfanin sumunti mai zaman kansa da kwangila ta binciko rinjiyoyin mai guda 18 da rijiyoyin sauran ma’adinai kimanin dubu daya. Wannan kuwa ba kome ba ne illa tukwici ga wadanda suka rika ba shi goyan baya tsawon mulkinsa na shekaru takwas.”

To daga Nijeriya zamu juya zuwa ga makobciyarta Nijer, wadda ga alamu ta fara fuskantar wata barazana ta ‘yan tawaye na Tuareg a yankinta na hamada, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito ta kuma kara da cewar:

“Kasar Nijer dai a halin yanzu haka ita ke sayarwa da Kungiyar Tarayyar Turai kashi 13% na ma’adanin Uranium da take bukata, kuma daga baya-bayan nan ta rattaba hannu kan wata yarjejeniyar binciko karin adanin ma’adanin na Uranium da wani kamfanin ma’adinai na kasar Kanada, a baya ga wasu yarjeniyoyin dake tsakaninta da kasashen China da Indiya da kuma Birtaniya. A daura da Uranium Allah Ya fuwace wa Nijer man fetur da wasu ma’adinan kamar yadda ake kyautata zato. Amma a sakamakon hare-haren ta’addanci na baya-bayan nan a Aljeriya da kuma kafa wata kungiyar al-Ka’ida ta yankin Magreb da aka yi hade da matakan ‘yan tawaye a cikin kasar Nijer kanta ya sanya yankin Sahel cikin rukunin yankunan da ba su da kwanciyar hankali. Amma ita gwamnati ta dage akan cewar bata da ‘yan tawaye sai dai gungu na ‘yan fashi da makami da masu safarar miyagun kwayoyi da ragowarsu.”

A cikin watan nan na yuni ne za a fara cin shari’ar tsofon shugaban Liberia Charle Taylor bisa zarginsa da laifukan amfani da arzkin ma’adinai don goya wa yake-yake guda biyu baya, a kasarsa ta Libetiya da kuma makobciyarta Saliyo. Wadannan yake-yake, kamar yadda jaridar Die Welt ta nunar sun yi sanadiyyar rayukan mutane sama da dubu 300 a baya ga ta’asa iri daban-daban da aka nuna wa farar fula. Abin madalla a baya ga wannan shari’a shi ne yadda kasar ta Liberiya ke farfadowa a cikin gaggawa fiye da yadda aka yi zato a karkashin shugaba Ellen Johnson Sirleaf.