1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

April 7, 2006

Ziyarar Köhler a Afurka ita ce ta dauki hankalin Jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/Bu0k
Köhler a Afurka
Köhler a AfurkaHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

A wannan makon ma jaridu da mujallun Jamus sun fi mayar da hanakli ne ga ziyarar da shugaban kasar Jamus Horst Köhler ke yi yanzu haka ga kasashe uku na nahiyar Afurka, wadanda suka hada da Muzambik da Madagaskar da Botswana. Jaridar RHEINISCHE POST tayi amfani da wannan dama domin bitar halin da kasashen guda uku ke ciki sai ta ci gaba da cewar:

“Shugaban kasar Jamus Horst Köhler ba bako ban e a nahiyar Afurka. Bugu da kari kuma a yayinda wasu ke watsi da makomar nahiyar sakamakon matsalolinta na yakin basasa da talauci, shi shugaban yayi matukar damuwa ne wajen ganin kasashen Afurka sun farfado domin a rika damawa dasu a harkoki nay au da kullum a wannan duniya tamu. Wannan kuma shi ne karo na biyu da ya kai ziyara Afurka a matsayinsa na shugaban kasar Jamus. Niyyarsa kuwa it ace ya rika kai ziyara nahiyar a kowace shekara, ko da yake a bara bai samu ikon yin haka ba sakamakon zabe na gaba da wa’adin da aka gudanar a nan Jamus. Zangonsa na farko kuwa it ace Muzambik, inda bayan shekaru 16 na yakin basasa a yanzu sassan da suka gwabza wannan yakin sun mayar da majalisar dokoki dandalin mahawara domin neman bakin zaren warware matsalolinsu. Kuma tun bayan da shugaba Armande Guebuaza ya dare kan karagar mulki sakamakon zabe na demokradiya karshen shekara ta 2004 kasar ke bakin kokarinta wajen yaki da cin hanci da miyagun laifuka a karkashin matakai na garambawul da gwamnati ke dauka. Ita ma Madagaskar, bayan matsaloli na siyasa da ta sha fama dasu sakamakon zaben shekara ta 2002 a yanzu al’amura sun sarara kuma shugaba Marc Ravalomanana na samun goyan baya daga kasashen ketare akan manufofinsa da suka shafi gyara ga kasafin kudin kasa da mayar da kamfanonin gwamnati ga ‘yan kasuwa masu zaman kansu. Ita kuwa Botswana dama tuni ta zama abar misali tsakanin kasashen Afurka dangane da irin ci gaban da take samu inda take amfani da ribar da take samu daga cinikin albarkatun kasa domin daga matsayin tattalin arziki da kuma kyautata jin dadin rayuwar al’umarta.

Matsalar cin hanci ta zama rowan dare a kasar Kenya abin day a hada hard a cibiyar shugabancin kasar in ji jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG wadda ta ci gaba da cewar:

“Tare da alkawarin yaki da cin hanci ba sani ba sabo shugaba Kibaki ya samu nasarar darewa kan karagar mulki sakamakon zaben da aka gudanar a shekara ta 2002 domin mayewa gurbin tsofon shugaba Daniel arap Moi, wanda yayi tsawon shekaru 24 yana mulki. Amma a yanzun an wayi gari murnar al’umar kasar Kenya ta koma ciki sakamakon tabargazar cin hanci iri daban-daban, wadanda aka ce sun shafi abin day a kai Euro miliyan dubu kuma ana kyautata zaton cewar ita kanta fadar shugaban tana da hannu dumu-dumu a wannan tabargaza. Tuni kafofin bad a lamuni na kasa da kasa suka dakatar da taimakon da suke ba wa Kenya su kuma kasashen Turai na tunanin kakaba takunkumi akan jami’an siyasar kasar domin haramta musu kawo ziyara cikinsu.”

Ko da yake an samu sararawar al’amura a yankin Nigerdeltan Nijeriya, amma kasashe sun damu matuka ainun a game da hali na dardar da yankin ke fama da shi, wanda zai iya yin mummunan tasiri akan farashin mai a kasuwannin duniya, in ji Jaridar DER TAGESPIEGEL, wadda ta kara da bayanin cewar:

“Nigeriya ce a matsayi na takwas tsakanin kasashen dake cinikin mai a kasuwannin duniya, inda take hako abin day a kai garewani miliyan biyu da dubu 600, kuma akasarin man ana hako shi ne a yankin Delta. A sakamakon haka duniya ta damu matuka ainun a game da halin da ake ciki a wannan yanki saboda tasirinsa akan farashin maid a kuma makomar tattalin arzikin ita kanta Nijeriya.”