1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

September 14, 2007

Har yau Zimbabwe na ci gaba da daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvP7

Ko da yake a wannan makon ganawar da aka gudanar a fadar Vatikan tsakanin Paparoma Benedikt na 16 da shugaba Al-Bashir na kasar Sudan ita ce ta fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a daf da karshen mako, amma a daya bangaren ba su yi sako-sako da abubuwan dake faruwa a sauran sassa na nahiyar Afurka ba, kamar dai misali kasar Zimbabwe, inda jaridar Die Welt ke cewar idan ba a hamzarta aka kai mata doki ba to kuwa zata wargaje kwata-kwata, saboda a halin yanzu haka kasar na fama da karancin abinci da ruwan sha mai tsafta da rashin wutar lantarki a biranenta. Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung bayan da tayi bitar halin da ake ciki a Zimbabwe da kuma famar kai ruwa ranar da ake yi dangane da manufofin shugaba Robert Mugabe sai ta saka ayar tambaya a game da cewar ko shin taron kolin da aka shirya gudanarwa tsakanin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da ta Gamayyar Afurka zai ci tura sakamakon sabanin da ake yi akan shugaban na kasar Zimbabwe? Jaridar ta kara da cewar:

“A dai halin da ake ciki yanzun ba wanda ya san ko shin shugaba Robert Mugabe zai tsayar da wata shawara ta radin kansa ya ki halartar zauren taron kolin da aka shirya gudanarwa tsakanin KTT da ta tarayyar Afurka nan gaba a wannan shekara. A hukumance dai tilas ne a gayyaci dukkanin kasashen Afurka zuwa zauren taron ba zata yiwu a mayar da wata kasa saniyar ware ba. Kuma rahotanni daga Brussels sun nuna cewar shugaba Mugabe na da goyan bayan akasarin kasashen Afurka a game da halartar taron. Baban dalilin haka kuwa shi ne farin jinin da yake da shi a matsayin daya daga cikin baraden faman neman ‘yancin kasashen Afurka. A baya ga haka babu wata dokar dake haramta masa halartar taron. Duka-duka abin da za a yi shi ne ita KTT ta takunkumin hana shigowa kasashenta da ta kakaba masa.”

A can kasar Kongo ga alamu al’amura zasu sake dagulewa, domin kuwa a daidai lokacin da ake samun sararawa sakamakon yarjejeniyar tsagaita wutar dake ci tsakanin sojojin gwamnati da dakarun Madugun ‘yan tawaye Nkunda, makobtan kasar sun fara raba kawunansu domin rufa wa sassan da basa ga macijin baya. A yayinda kasashen Uganda da Angola ke goya wa gwamnati baya ita kasar Ruwanda sai ta koma bangaren ‘yan tawayen. Jaridar Die Tageszeitung ce ta nuna hakan ta kuma kara da cewar:

“Jita-jita sai dada yaduwa take yi a game da yiwuwar fuskantar arangama tsakanin sojojin Uganda da na Ruwanda a gabacin Kongo. Hakan ya jefa mutane cikin rudu da rashin sanin tabbas tare da tsoron kada fa tawayen Nkundua ya yadu zuwa sauran sassa na kasar. Kasar Ruwanda dai ita ce ta sa baki aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ‘yan tawayen Nkunda da gwamnatin kongo a wajejen karshen shekara da ta gabata, a saboda haka makomar yarjejeniyar ta danganta ne da irin rawar da Ruwanda zata taka nan gaba.”

A sakamakon ganawar da aka shirya a wannan makon tsakanin Paparoma Benedikt na sha shida da shugaba Al-Bashir na kasar Sudan Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi amfani da wannan dama domin bitar dangantakar fadar Vatikan da kasar Sudan mai musulmi a arewaci da kiristoci a kudancinta jaridar ta ce.

“A hakika sabani tsakanin bangaren Musulmi na kasar Sudan da mujami’a a Rome yana da dadadden tarihi daidai da tarihin ita kanta Sudan. Domin kuwa tun a cikin karni na 6 ne addinin kirista ya shiga yankin Nubiya na kasar Sudan, amma daga bisani musulunci ya yadu a cikinsa. Bayan mamayar da Turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka yi wa Sudan a wajejen karshen karni na 19, Birtaniyar ta bai wa ‘yan mishan damar yada addinin kirista a kudanci a yayinda arewacin Sudan ta ci gaba da kasancewa karkshin rinjayen musulmi. To sai dai kuma ba maganar addini ne kadai ummal’aba’isin rikici tsakanin arewaci da kudancin Sudan ba, akwai sauran batutuwa na siyasa da tattalin arziki dake taka muhimmiyar rawa a wannan rikici”.