1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

September 7, 2007

Ziyarar Ban Ki Moon zuwa Sudan da Cadi ita ce tafi daukar hankalin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvP8

A wannan makon dai ko da yake ziyarar da sakatare-janar na MDD Ban Ki Moon ya kai a yankunan da ake fama da rikici a cikinsu na Sudan da Chadi ita ce tafi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon, amma ba su yi watsu da irin ci gaban da ake samu a sauran sassa na nahiyar Afurka ba. Misali halin da ake ciki a gabacin kasar Kongo. Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“A gabacin Kongo ana fuskantar barazanar sake barkewar fada sakamakon musayar wutar da ta wakana baya-bayan nan tsakanin sojojin gwamnati da dakarun janar Laurent Nkunda dake tawaye. Wannan rikicin da ake fama da shi tare da Laurent Nkunda wata kyakkyawar alama ce a game da gaskiyar cewa ba a taba samun zaman lafiya ba a gabacin Kongo kuma shi kansa zaben da aka gudanar a kasar shekarar da ta wuce ya gaza akan wannan manufa.”

A wannan makon sakatare-janar na MDD Ban Ki Moon ya kai ziyarar bin bahasi akan halin da ake ciki a lardin Darfur na yammacin Sudan da kuma makomar zaman lafiyar yankin kudancin kasar. A lokacin da take tofa albarkacin bakinta akan wannan ziyarar jaridar Süddeitsche Zeitung cewa tayi:

“MDD ta bata lokaci matuka ainun tana mai bin manufofin diplomasiyya domin tsugunar da sojojin kiyaye zaman lafiya a lardin Darfur, a maimakon mayar da hankali wajen shawo kan rikicin a siyasance. Ga alamu dai dalilin haka shi ne kasancewar tura sojojin kiyaye zaman lafiyar na da nasaba da wata manufa ta nuna kasaita fiye da manufofi na diplomasiyya, musamman ma dangane da kasar Sudan, wadda al’amuranta ke da sarkakiyar gaske. Amma fa wani muhimmin abin da zai taimaka a cimma nasara wajen tinkarar rikicin a siyasance shi ne hadin kai da kasar China.”

Dangane da rawar da kasar China ke takawa a nahiyar Afurka jaridar Finincial Times ta Jamus tayi sharhi tana mai cewar:

“Sannu a hankali kasar China na iza keyar kasashen Turai domin su canza salon kamun ludayinsu a ma’amallarsu tare da kasashen Afurka. Ganin yadda kasar ta China take ba da cikakken hadin kai ga kasashen Afurka ya sanya su ma kasashen Turai sun fara tunanin yin hakan, inda kantomar hukumar zartaswa ta Kungiyar Tarayyar Turai akan manufofin ketare Banita Farrero Waldner take ganin wajibi ne a gayyaci kasar Zimbabwe domin halartar taron kolin da aka shirya gudanarwa nan gaba a wannan shekarar tsakanin kasashen Turai da na nahiyar Afurka. Tuni ma gwamnatin Birtaniya ta fara nuna amincewarta da wannan shawara saboda tsoron ka da watan-wata rana a wayi gari kasashen na Turai sun zama ‘yan rakiya ne kawai a dangantaka da makobtansu na Afurka.”

A wata tabargaza ta mahukunta a kasar Turkiyya an kashe wani dan Nijeriya a lokacin da yake tsare a gidan wakafi. Jaridar Die Tageszeitung ce ta rawaito wannan rahoto ta kuma kara da cewar:

“A karshen makon da ya gabata ‘yan sanda a birnin Istamnbul na kasar Turkiyya suka tsare wani dan Nijeriya bisa tuhumarsa da cinikin hodar iblis. A kuma yayin da yake tsare a gidan wakafi aka bindige shi har lahira, ko da yake mahukunta sun yi ikirarin cewar wai fada ne ya kaure tsakaninsa da wani dan sanda kuma a kokarinsa na kwace bindiga daga hannun dan sandan ne bindigar ta harba shi kuma ya halaka nan take. Wannan labarin ya fito fili ne sakamakon zanga-zanga da bakar fata ‘yan Afurka suka gudanar a titunan Istanbul karshen mako.”