1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

June 29, 2007

Maganar shawo kan rikicin Darfur shi ne ya fi daukar hankalin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPF

Halin da ake ciki a lardin Darfur na yammacin kasar Sudan shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus tare da ba da la’akari da taron da kasar Faransa ta kira domin nazarin hanyoyin neman zaman lafiyar lardin a farkon wannan makon. Amma zamu fara ne da wasu rahotanni guda biyu da jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga dangane da Nijeriya. Rahotonta na farko a farko-farkon wannan makon ya danganci karar da aka daukaka ne akan kamfanin magungunan nan na Pfizer, wanda ake zargi da amfani da yara kanana domin gwajin wasu magunguna da ta kirkiro, wadanda ko dai sun halaka yaran kwata-kwata ko kuma sun gurgunta su baki daya. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Wasu litattafai na almara dake batu a game wani kamfanin sarrafa magunguna, wanda a sakamakon kwadayin samun kazamar riba ya rika amfani da yara kanana a nahiyar Afurka wajen gwajin magungunansa.” Jaridar ta ce ko da yake wannan almara ce, amma sai ga shi ta tabbata gaskiya, kuma daramar ta yanzu ta shafi gwajin magunguna ne akan yaran da a yanzu haka suke fama da radadin lamarin, wanda a daya bangaren ya shafi dubban miliyoyi na dalar Amurka. Gwamnatin Nijeriya na nema daga kamfanin Pfizer da ya biya diyyar dalar Amurka miliyan dubu bakwai saboda yayi gwajin magungunan akan yara da sauran majiyyata ba tare da cikakken izini ba, wadanda kuma tun bayan wannan gwaji a shekara ta 1996 suke fama da munanan radadi.”

A cikin daya rahoton nata dangane da Nijeriya jaridar ta Düddeutsche Zeitung ta duba halin da ake ciki ne a yankin Niger Delta, inda take cewar:

“A cikin watanni 12 da suka wuce ‘yan ta da zaune tsaye sun yi garkuwa da sama da mutane dari ‘yan kasashen ketare suka kuma tilasta aka rufe wasu rijoyoyin hakan mai a yankin Niger Delta. A sakamakon wannan ta da zaune tsaye yawan mai da Nijeriya ta saba haka ya samu koma bayan kashi daya bisa hudu. Sabon shugaban Nijeriya Umaru Musa ‘yar Adua na bakin kokarinsa wajen shiga shawarwari da ‘yan ta kifen, kuma domin nuna kyakkyawar niyyarsa game da wannan manufa ya sa aka saki madugun ‘yan ta kife Dokubo Asari daga gidan kurkuku. A halin yanzun dai shugaban na fafutukar kafa wata gwamnati ta hadin kan kasa, mai yiwuwa idan hakan ta tabbata a samu kafar tsamo Nijertiyar daga cikin mawuyacin hali na tabarbarwar al’amuran tsaro a kasar.”

Kasar Faransa na fatan rufa wa MDD baya a kasashen Chadi da Sudan. Wannan shi ne kanun wani rahoton da jaridar Die Tageszeitung ta rubuta a game da fafutukar da sabuwar gwamnatin Faransa take yi domin ganin an samu sararawar al’amura a kasashen Chadi da Sudan, inda al’amura ke dada tabarbarewar sakamakon rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a lardin Darfur. Jaridar ta Die Tageszeitung ta kara da cewar:

“Wannan zai kasance karo na farko da kasar Faransa ta shigar da sojojinta karkashin tutar MDD domin aikin kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afurka. Domin kuwa kawo yanzu kasar ta kan yi gaban kanta ne ko kuma shiga tutar Kungiyar Tarayyar Turai a matakan kiyaye zaman lafiya a nahiyar.”

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

“Kasar Sudan dai bata halarci zauren taron Darfur da Faransa ta kira a farkon wannan makon ba. Kuma ko da yake fadar mulki ta Khartoum tayi na’am da shawarar tsugunar da rundunar hadin guiwa ta MDD da Kungiyar Tarayyar Afurka ta AU, amma ba wanda ya san lokacin da za a tsugunar da wannan runduna ta kiyaye zaman lafiya. Bugu da kari kuma alkawarin da Faransa tayi ya haddasa rudami a shelkwatar MDD, domin kuwa hakan na iya sanya al’amura su kara tabarbarewa a maimakon fatan da ake yi na shawo kan rikicin a siyasance.”