1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

November 10, 2006

Amfani da maganar cin hanci a siyasar Nijeriya na daga cikin abubuwan da jaridun Jamus suka yi sharhi akansa

https://p.dw.com/p/BvPX

Shirin na yau zai fara ne da wani dogon sharhin da jaridar FRAKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta rubuta a game da siyxasar Nijeriya, inda ta ce tuni maganar cin hanci ta zama wani babban makami a yakin neman zaben kasar da za a gudanar shekara mai zuwa. Jaridar ta ci gaba da cewar:

“Hukumar yaki da cin hanci da EFCC, ita ce babban makami bisa manufa. To amma abin lura a nan shi ne kasancewar hukumar ta fi mayar da hankalinta ne ga ‘yan siyasar da basa ga maciji da shugaba Obasanjo ko kuma ake hangen cewar suna iya zama kalubala ga shugaban mai ci a yanzu. Domin kuwa idan aka ajiye maganar mataimakin shugaba Obasanjo, Abubakar Atiku gefe guda za a ga jerin gaggan ‘yan siyasa da hukumar ta EFCC ke tinkararsu daya bayan daya wadanda basa shiri da Obasanjo. Misali gwamnan jihar Anambra Peter Obi dan jam’iyyar Apga, babbar abokiyar gabar PDP ta shugaba Obasanjo, wanda a makon da ya gabata aka kakkabe shi daga mukaminsa. Kaddarar da ta rutsa da Peter Obi ana iya kwatanta ta tamkar wani mataki na ci da ceto ne Obasanjo ya dauka kansa, domin ganin ya fice daga tutar Apga ya koma karkashin tutar PDP.”

A ci gaba da bitar matsalar cin hanci a wannan makon kaddara ta rutsa da wani kamfanin Jamus mai suna Lehmeyer, inda bankin duniya ta dakatar da kwangilarsa saboda laifuka na ba da toshiyar baki. A lokacin da take ba da rahoto akan haka jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU cewa tayi:

„Bayan bincike mai zurfi da ya gudanar bankin duniya ya gano cewar kamfanin Lehmeyer ya ba da toshiyar baki ga Masupha Sole domin samun kwangilar wani shiri na samar da ruwa a kasar Lesotho. Masupha Sole shi ne manajan wannan shiri, wanda ke da nufin samar da ruwa mai tsafta ga wasu yankuna na Afurka ta Kudu da kuma wutar lantarki a kasar Lesotho. A wajejen karshen shekarun 1990 ne aka fallasa wannan mummunar manufa ta ba da cin hanci da kamfanin Lehmeyer yayi tare da wasu kamfanonin guda uku, sakamakon wani binciken da bankin duniya ya gudanar a Afurka.“

Ita kuwa jaridar GENERAL-ANZEIGER a cikin nata sharhin tayi ikirari ne cewar kasar China na barazana ga makomar mulkin demokradiyya a nahiyar Afurka, inda ta ci gaba da cewar:

„Murna fa tana neman komawa ciki bayan kyakkyawan ci gaban da aka samu na kadawar iskar demokradiyya a nahiyar Afurka, wadda ta kai ga kirkiro kungiyar nan ta NEPAD dake da nufin karfafa mulkin na demokradiyya a wannan nahiya. Domin kuwa a yanzun China na neman yin banakere a al’amuran Afurka ba tare da gindaya sharudda ba a kokarinta na neman sabbin abokan huldar ciniki da kwadayin albarkatun kasa da Allah Ya fuwace wa nahiyar.“

Ita ma jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG ta yi bitar wannan sabon ci gaba inda take cewar:

„Yadda kasar China mai angizon tattalin arziki ke fafutukar yin babakere a nahiyar Afurka a cikin gaggawa abu ne mai ban tsoro. A cikin shekaru goma kacal an samu ribanyar huldar cinikayya tsakanin China da kasashen Afurka har niniki goma. A kuma lokacin taron kolinsu a Peking Chinar tayi wa shuagabannin Afurka alkawururrukan na taimakon dubban miliyoyin dala, wadanda su kansu kasashe mawadata dake da ci gaban masana’antu ba zasu iya bayarwa ba. Ko da yake a bangare guda ana iya madalla da wannan ci gaba saboda yana iya zama wata kyakkyawar dama ga kasashen Afurka domin fita daga kangin talauci, amma a daya bangaren idan aka waiwayi baya za a ga shuagabannin na Afurka basa amfani da wadannan kudade domin ta da komadar tattalin arzikin kasa da kyautata rayuwar al’umarsu.“