1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

November 3, 2006

Barazanar dake tattare da zirga-zirgar jiragen sama a Afurka na daga cikin batutuwan da suka shiga kanun rahotannin Jamus

https://p.dw.com/p/BvPY

A yau sharhin jaridun na Jamus zai fara ne da rahoton jaridar DIE WELT akan hadarin dake tattare da zirga-zirgar jiragen sama a nahiyar Afurka. Jaridar ta ci gaba da yin nuni da cewar:

“Tun bayan wata ‘yar tangardar da aka fuskanta a garin goma na kasar Kongo a cikin watan mayun shekara ta 2005, lokacin da wani jirgin dake dauke da ministocin tsaro na wasu kasashen Afurka guda hudu ya ci karo da wani shinge a lokacin da yake kokarin tashi, ya zuwa halin da muke ciki yanzu sama da fasinjojin jiragen sama 400 suka yi asarar rayukansu sakamakon hadarurukan jiragen, galibi kuwa a Nijeriya, inda a karshen makon da ya wuce aka sake fuskantar wani hadarin jirgin. Alkalumar hukumar sufurin jiragen sama ta kasa da kasa sun nuna cewar Afurka ce ke da rabo na kashi daya bisa uku na illahirin hadarurrukan jiragen sama dake faruwa a sassa daban-daban na duniya.”

Ita kuwa jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG ta duba ci gaban da ake samu ne a fafutukar yaki da matsalar talauci, inda ta ce bunkasar tattalin arziki na taimakawa wajen yakar wannan matsala a nahiyar Afurka. Jaridar dai ta kara da bayani tana mai cewar:

“Kasashe da dama na Afurka na samun kyakkyawan ci gaba a matakansu na yaki da matsalar talauci. A halin yanzu haka akwai kasashe 16 na wannan nahiya wadanda ke samun bunkasar da ta zarce ta kashi 4.5% ga tattalin arzikinsu a shekara tun abin da ya kama daga tsakiyar shekarun 1990. Wadannan kasashe kuwa sun hada da Senegal da Muzambik da Burkina Faso da Kamaru da Uganda da Ghana da kuma Cap Verde. Dukkan wadannan kasashen suna samun bunkasar da tayi daidai da ta sauran kasashe masu tasowa a sassa daban-daban na duniya.”

To sai dai kuma a daya bangaren akwai wasu kasashen dake fama da tafiyar hawainiya musamman sakamakon matsaloli na fari in ji jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG wadda ta ba da misali da kasar Habasha, jaridar sai ta ce:

“Wani bayanin da aka samu daga wata kungiyar kare kewayen dan-Adam ta kasar Birtaniya ya nuna cewar yankunan dake fama da fari da karancin ruwan sama a nahiyar Afurka zasu kara shiga halin kaka-nika-yi, a yayinda su kuma masu samun ruwan saman al’amura zasu dada kai musu iya wuya sakamakon canje-canjen yanayin da ake fuskanta. Dangane da kasa kamar Habasha kuwa abin zai haifar mata da mummunan sakamako. Sama da mutane miliyan 25 a yankunan Afurka dake kudu da hamadar Sahara suka dogara kacokam akan taimakon abinci daga ketare, musamman kuwa a yankunan Habasha da Somaliya da Jibuti da kuma arewacin Kenya. A wadannan yankuna a baya ga matsaloli na yanayi ana kuma fata da rikice-rikice tsawon shekaru da dama da suka wuce.”

Wani hamshakin dan kasuwar kasar Sudan dake zaune a birnin London yayi wa shuagabannin Afurka tayi ta gomashi, inda ya ce zai ware tsabar kudi dalar Amurka miliyan biyar da zai ba da su kyauta ga duk wani shuagaban kasar da ya bar kujera bisa radin kansa bayan tafiyar da mulki na adalci da tinkarar matsalar talauci dake addabar al’umarsa. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU cewa tayi:

“Bisa ga ra’ayin Mo Ibrahim, hamshakin dan kasuwar Sudan dake da zama a birnin London, akasarin shuagabannin Afurka ba sa kaunar barin gadon mulki bisa radin kansu saboda more rayuwar da suke yi. A saboda haka ya tsayar da shawarar kafa wani kwamitin da zai kunshi gaggan masana 18 wadanda zasu rika bita domin zaben shuagabannin da suka cancanci samun wannan kyauta ta yabo ga salon mulki na gari.”