1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

September 29, 2006

Zaben kasar Zambiya ya dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPd

Zaben kasar Zambiya na daga cikin batutuwan da masharhanta na jaridun Jamus suka mayar da hankali kansa tare da ba da la’akari da matsalar da ta dabaibaye yakin neman zaben. A cikin nata sharhin jaridar DIE TAGESZEITUNG cewa tayi:

“Babban abin da jami’an hamayyar kasar Zambiya suka fi mayar da hankalinsu akai a yakinsu na neman zabe shi ne fatattakar Sinawa da Kwarori da kuma Indiyawa daga harabarb kasar in har sun samu nasarar zaben. Domin a ganinsu wadannan ‘yan kaka-gida sune ke handume dukiyar kasar a yayinda su kuma sauran talakawa suke ci gaba da fama da radadin talauci.”

Tun bayan da dakarun tarayyar kotunan musulunci ta kasar Somaliya ta mamaye birni na uku mafi girma a kasar Somaliya ake fama da takun saka tsakaninta da kasar Habasha. A lokacin da take sharhi akan haka jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

“Ko da yake kasar Kenya dake karbar dimbim ‘yan gudun hijirar Somaliya a harabarta, tayi godo ga sassan biyu da su nuna halin sanin ya kamata, amma ga alamu tuni kasar Habasha ta kuduri niyyar saka kafar wando daya da kungiyar mai zazzafan ra’ayin akidar addini a kasar Somaliya. A ganin shuagabannin kasar Habasha kungiyar fafutuka take yi na sake mamayar yankin Ogaden dake kunshe da Somaliyawa a karkashin tutar Habasha.”

A wannan makon ministan tsaron Jamus Franz-Josef Jung yayi fatali da kiran da ake yi na kara wa’adin aikin sojan kiyaye zaman lafiya na kasar a Janhuriyar Demokradiyyar Kongo. A lokacin da take bayani game da haka jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG har ila yau cewa tayi:

“Ba tare da wata rufa-rufa ba ministan tsaro Franz-Josef Jung yayi fatali da kiraye-kiraye da ake yi game da kara wa’adin aikin sojan kiyaye zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar Turai a kasar Kongo, inda ya ce MDD da majalisar dokoki ne suka bukaci tsugunar da sojojin har ya zuwa 30 ga watan nuwamba mai zuwa kuma maganar kara wa’adin ko da ta rana daya ce ba ta taso ba.”

Kimanin ‘yan gudun hijirar Afrika miliyan biyu suka ya da zango a kasar Spain a cikin shekaru biyar din da suka wuce, inda wasu daga cikinsu kan yi kaka gida wasu kuma su kara gaba, in ji jaridar DIE ZEIT a cikin wani dogon sharhin da ta rubuta ta kuma ci gaba da cewar:

“A wannan shekarar kadai tun abin da ya kama daga watan janairu zuwa karshen watan agusta bakin haure kimanin dubu 19 da 35 daga kasashen Afurka suka sauka tsuburan kanariya na kasar Spain. A wani garin da ake kira Yoff a kasar Senegal ana iya lura da yadda kananan kwale-kwalen kamun kifi ke daukar fasinja daga sassa daban-daban na Afurka domin kama hanyar shigowa Turai akan Euro 500. Wanda kazamar riba ce ga masu kamun kifin musamman ma ganin irin matsalolin da suke fuskanta a halin yanzu sakamakon kalubale daga manyan jiragen ruwan kamun kifi daga kasashen Turai.”