1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

August 25, 2006

Halin da ake ciki a Kinshasa na ci gaba da daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/BvPg
Tashin hankula a Kinshasa
Tashin hankula a KinshasaHoto: AP

Babban abin da ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon dai shi ne halin da ake ciki dangane da karuwar yawan ‚yan gudun hijira na Afurka dake kokarin shigowa nahiyar Turai ko ta halin kaka. A lokacin da take gabatar da rahotonta akan wannan matsala jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG cewa tayi:

„Duk da daruruwan ‚yan gudun hijirar da aka kiyasce cewar sun yi asarar rayukansu a wannan shekarar, amma duk da haka bayanai masu nasaba da kungiyar Red Cross ta kasar Spain sun ce a halin yanzu haka akwai sama da ‚yan Afurka dubu dari dake zaman tsammanin warrabbuka a kokarinsu na shigowa Turai a can kasar Senegal, wadda daga baya-bayan nan ta sake nanata kira ga kasashen Kungiyar Tarayyar Turai da MDD da su taimaka mata wajen tinkarar wannan matsala dake nema ta zame mata gagara-badau. Tun dai abin da ya kama daga farkon wannan shekarar zuwa yanzun ‚yan gudun hijirar Afurka sama da dubu 18 ne suka kutsa tsuburan kanariya na kasar Spain galibi daga kasashen Mauritaniya da Senegal.“

A cikin wani sabon ci gaba a can gabar tekun kasar Somaliya dakarun kungiyar Musulmi mai zazzafar akida sun samu nasarar karya alkadarin ‘yan fashin jiragen ruwa bayan da kasashen yammaci suka gaza duk da manyan jiragen ruwansu na yaki dake da damarar muggan makamai, kamar yadda jaridar NEUES DEUTSCHLAND ta rawaito ta kuma kara da cewar:

„Akalla an fuskanci hare-hare na ‚yan fashin jiragen ruwan har sau 41 a tun abin da ya kama daga watan maris na shekarar da ta wuce, duk kuwa da manyan jiragen ruwa na yaki daga kasashen yammaci dake sintiri a gabar tekun kasar Somaliya. A wajejen karshen watan yulin da ya wuce shugaban kungiyar majalisar shura ta musulmin Somaliya Sheikh Hassan Tahir Uwais ya lashi takobin saka kafar wando daya da ‚yan fashin. Ga alamu kuwa an cimma biyan bukata sakamakon mamayar shelkwatar ‚yan fashin da dakarun kungiyar suka yi a yankin Harardere mai tazarar kilomita 400 daga birnin Mogadishu.“

A wannan makon an ci gaba da fuskantar tashe-tashen hankula kamar yadda aka yi hasashe tun da farko dangane da sakamakon zaben da aka gudanar karshen watan da ya gabata. Jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG tayi karin bayani tana mai cewar:

„A sakamakon jita-jita da wasu batutuwan da ba su taka kara sun karya ba aka shiga wani mummunan yanayi na tashe-tashen hankula a Kinshasa, bayan zagayen farko na zaben shugaban kasa, inda a yanzun za a fuskanci zaben fid da gwani tsakanin Joseph Kabila da Jean-Pierre Bemba. Dangane da dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa da aka tsugunar kuwa, a wannan halin da ake ciki basu da wani iko na yin tasiri a lamarin.