1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

June 30, 2006

Makomar demokradiyya a Nijeriya na daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka yi sharhi akansu

https://p.dw.com/p/BvPp
Sojan EU domin tsaron zaman lafiyar Kongo
Sojan EU domin tsaron zaman lafiyar KongoHoto: AP

Duk da shagulgulan da ake yi dangane da gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a duk fadin kasar nan ta Jamus, amma jaridu da mujallunta ba su yi watsi da batutuwan nahiyarmu ta Afurka ba. Misali jaridar nan ta NEUES DEUTSCHLAND mai ra’ayin irin shigen na gurguzu tayi bita a game da makomar siyasar Nijeriya bayan saukar Obasanjo daga karagar mulkin kasar, inda ta ce ko da yake Nijeriya tana samun kyakkyawan ci gaba akan tsarin mulkinta na demokradiyya da ta gabatar tun shekara ta 1999, inda majalisar dattawan kasar ta sa kafa tayi fatali da shawarar canza daftarin tsarin mulki domin bai wa Obasanjo wata dama ta zarcewa akan karagar mulki, amma fa har yau kasar ta yammacin Afurka na fama da wahala wajen tabbatar da sahihin tsarin demokradiyya a cikinta. Jaridar sai ta kara da cewar:

“Ko da yake Obasanjo na da farin jini a ketare, musamman ma a kasashen yammaci, wadanda ke yaba wa matakansa na yaki da cin hanci da farfado da tattalin arzikin kasa, amma fa lamarin ba haka yake ba a cikin gida. Ta la’akari da haka kudurin da majalisar dattawan kasar ta yanke game da fatali da shawarar yi wa daftarin tsarin mulkin Nijeriya kwaskwarima ta yadda Obasanjon zai ci gaba da mulki abu ne da yayi daidai da ra’ayin akasarin al’umar kasar, kuma wannan wata gagarumar nasara ce ga makomar demokradiyya.”

Bisa ga dukkan alamu murna zata koma ciki dangane da shawarwarin neman zaman lafiyar Lardin Darfur, bayan da kungiyar SLA ta ce ta kakkabe hannuwanta daga yarjejeniyar zaman lafiyar da aka ba da sanarwa kanta a karshen watan mayun da ya gabata, kazalika da sabanin da ake fama da shi tsakanin Sudan da MDD, in ji jaridar DIE TAGESZEITUNG wadda ta ci gaba da cewar:

“Bisa ga dukkan alamu kungiyar SLA ta bijire wa yarjejeniyar ta zaman lafiya ne sakamakon kiyawa kememe da gwamnatin Sudan ke yi a game da bai wa MDD cikakkiyar dama ta taka muhimmiyar rawa a ayyukan tsaron zaman lafiyar Darfur, duk kuwa da cewar wannan manufa wani bangare ne na yarjejeniyar zaman lafiyar. A dai halin yanzu haka lalube ake yi a cikin dufu ba a san yadda za a sake billo wa lamarin ba.”

Kwararrun masana na kungiyar UNICEF sun gabatar da gargadi a game da wata arangamar da ka taso a Kongo inda zai zama wajibi akan sojan kiyae zaman lafiya na Kungiyar Tarayyar turai su bude wuta akan kananan yara dake cikin damarar makamai. A lokacin da take rawaito wannan rahoto jaridar DIE WELT cewa tayi:

“Makonni kalilan kafin fara aikin sojan kiyaye zaman lafiya na kasashen KTT a kasar Kongo kwararrun masana sun fara gargadi a game da yiwuwa fuskantar bata kashi tsakanin sojojin da kananan yara dake cikin damarar makamai. An dai kiyasce cewar a kasar Kongo akwai yara kimanin dubu 18 dake cikin damarar makamai. Wadannan yara ko da yake su kansu suna cikin kaka-nika-yi, amma fa a daya bangaren suna iya zama barazana ga sojojin. Shi dai kwamandan rundunar ta kiyaye zaman lafiya janar Karlheinz Viereck ya ce a bisa ka’ida sojojin na da ikon bude wuta akan kananan yaran dake cikin damarar makamai muddin sun fuskanci barazana daga garesu.”