1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

May 12, 2006

Kasar ghana na samun bunkasa sakamakon zaman lafiya da kwanciyar hankali

https://p.dw.com/p/BvPt

Zamu dai fara ne da rahoton da jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta buga a game da kasar Ghana, wadda ta ce ta zama abin misali a game da zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin kasashen Afurka. Jaridar dai cewa tayi:

“A yayinda makobtanta Togo da Cote d’Ivoire, wadanda dukkansu suka cancanci shiga gasar karshe ta cin kofin kwallon kafa ta duniya, suke fama da rikice-rikice na siyasa ita Ghana Allah Yayi mata gyadar dogo inda al’umarta ke tafiyar da al’amuransu na rayuwa a cikin lumana da kwanciyar hankali. Bayan da a zamanin baya kasar ta sha fama da juye-juyun mulki na soja a cikin shekaru na 1960 da 1970, a yau sai ga shi ta wayi gari tamkar abin misali a tsakanin kasashen Afurka, inda take bin wani nagartaccen tsarin mulki na demokradiyya da girmama ‘yancin ‘yan jarida. Kasar na samun ci gaban tattalin arziki na misalin kashi shida cikin dari a shekara kuma ta samu kafar kayyade matsalar hauhawar farashin kaya daga kashi 26 a shekara ta 2003 zuwa kashi 12 cikin dari yanzu haka.”

Bayan kai ruwa ranar da aka sha famar yi a shawarwarin sasanta rikicin lardin Darfur na kasdar Sudan an cimma daidaituwa akan wata yarjejeniya ta zaman lafiya tsakanin gaggan bangarorin da rikicin ya shafa. To sai dai kuma jaridar GENERAL ANZEIGER a lokacin da take ba da rahoto a game da wannan ci gaba ta saka ayar tambaya a game da ko shin Ya-Allah za a aiwatar da yarjejeniyar kuwa. Jaridar sai ta ce:

“A dai halin da ake ciki yanzun ba wanda zai iya hasashe a game da ko shin a hakika yarjejeniyar zata yi aiki ta yadda lardin na Darfur zai samu zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ita yarjejeniyar dai an cimmata ne sakamakon matsin lamba daga kasashen Amurka da Birtaniya akan dukkan bangarorin dake da hannu a wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa.”

Ita ma jaridar DIE TAGESZEITUNG ta yi bitar lamarin inda take cewar:

“Bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar lardin Darfur mai fama da rikici a kasar Sudan a yanzun ba abin da ya rage illa maganar ba da kariya ga wannan yarjejeniya. Domin kuwa ko da yake kungiyar tarayyar Afurka na da dakarun sojanta su dubu bakwai a wannan yanki, amma duk da haka ba wani canjin da aka samu dangane da mawuyacin halin da jama’a ke ciki. A saboda haka kwararrun masana ke ganin wajibi ne MDD ta ba da gudummawar sojoji akalla dubu 20, lamarin da har yau aka kasa cimma daidaituwa kansa sakamakon adawa daga gwamnatin Sudan.”

Kasar Somaliya har yau tana fama da yamutsi duk da sabuwar gwamnatin da aka nada, wadda ga alamu take kame-kame amma ba ta da wani tasiri na a zo a gani, in ji mujallar DER SPIEGEL lokacin da take bitar halin da kasar ke ciki yanzu haka. Mujallar sai ta ci gaba da cewar:

“Kai tsaye bayan nadinsa da aka yi a matsayin sabon shugaban kasar Somaliya a Nairobin Kenya a shekara ta 2004 Abdullahi Yusuf Ahmed yayi kira ga MDD domin ta ba shi gudummawar sojan kiyaye zaman lafiya dubu 20 da zasu share masa hanyar kaiwa fadar mulki ta Mogadishu. Amma nan da nan muslmi masu tsananin kishin addini a kasar ta Somaliya suka lashi takobin saka damarar jihadi sakamakon niyyar da kasashen Uganda da Habasha suka nunar game da ba da gudummawar dakarunsu a rundunar ta MDD, kuma tun daga sannan tashe-tashen ke dada yin tsamari, inda ake fafatawa da dakarun kungiyar ta musulmi da wata kungiya mai kiran kanta wai gamayyar yaki da ta’addanci, wadda ke samun taimako daga gwamnatin Amurka.”